Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Rushe Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Ta Amurka - Trump

Trump ya nanata ikirarin da yayi a lokacin yakin neman zabensa na 2024 cewar FEMA ta kashe miliyoyin daloli cikin rashin adalci a martaninta ga mummunar guguwar da ta afkawa jihar North Carolina a watan Satumban da ya gabata, inda ta hallaka fiye da mutane 100.

A yau Talata, Shugaba Donald Trump ya kaddamar da sabon shiri akan hukumar tunkarar bala'o'i ta tarayyar amurka (FEMA), inda ya bukaci a rufe ta tare da mikawa daidaikun jihohi ayyukanta.

Trump, wanda ke kokarin rage yawan kashe kudaden gwamnati tun bayan hawansa kan karagar mulki a watan Janairun da ya gabata, ya wallafa da manyan baki a dandalinsa na sada zumunta mai suna Truth Social Platform cewar, FEMA karkashin jagorancin Biden ta kasance bala'i.

"Kamata yayi a rushe FEMA. Ta kasance maras karsashi kuma sannu a hankali ta daina aiki gaba daya. Kamata ya yi daidaikun jihohi su tunkari guguwa da makamantansu gwargwadon yadda suka zo. Ga alkinta kudi mai yawa ga kuma samar da sakamako !!! kamar yadda dan jam'iyyar Republican din ya kara bayyanawa

Trump ya nanata ikirarin da yayi a lokacin yakin neman zabensa na 2024 cewar FEMA ta kashe miliyoyin daloli cikin rashin adalci a martaninta ga mummunar guguwar da ta afkawa jihar North Carolina a watan Satumban da ya gabata, inda ta hallaka fiye da mutane 100.

FEMA wacce keda alhakin tunkarar bala'o'i sa'ilin da jihohin suka bukaci hakan, ta musanta zarge-zargen a wancan lokacin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG