Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Hutun Ranar Shugaban Kasa “Presidents' Day” A Amurka Ya Sauya


US Presidents Day Explainer
US Presidents Day Explainer

Babu wani bayani a game da murnar zagayowar maulidin haihuwar shi a Mount Vernon cikin bayanan da aka adana, yayin da kundin rubutun shi ya yi nuni da cewa shi haziki ne a faggen aiki.

Kamar sauran shugabannin(mutanen) da suka kafa Amurka, George Washington, baya sha'awar bayyana rayuwar shi a fili. Shi ne shugaban sabuwar jamhuriya na farko ba sarki ba.

A yau Litinin ne Amurkawa suke hutun ranar shugaban kasa na farko, shekaru 293 bayan haihuwar shi.

Ma'anar Ranar Shugabanni ta canza sosai, zuwa galibi abubuwa marasa amfani a wannan ranar da ya kamata a cike ta ayyuka na Washington na shekarun 1700, ba kasuwanci kayayyaki kamar yadda take a yanzu. Ga wasu masana tarihi, bikin ya rasa duk wata ma’ana da muhimmancinsa.

Masaniyar tarihi Alexis Coe kuma mawallafiyar “You Never Forget Your First,” wato wani littafi akan rayuwar tsohon shugaban Amurka George Washington, ta ce, a ra'ayin ta, Presidents' Day wannan dogon ginin da ke birnin Washington mai mahimmanci da ake kira da sunan shi.

An haifi Washington a ranar 22 ga watan Fabrairun 1732, a gonan Popes Creek kusa da Kogin Potomac a Jahar Virginia.

Ko da yake a zahiri, an haife shi ne a ranar 11 ga watan Fabrairu, bisa kalandar julian, wanda ake amfani da shi har tsawon shekaru 20 bayan lokacin haihuwar shi. Manufar Kalandar Gregorian shine a kamanta amfani da lissafin wata wanda aka kara wasu kwanaki 11 a kai da aka fara amfani da shi a shekarar 1752.

Duk da haka, Washington bai fiye damuwa da maulidn haihuwar shi ba, a bisa bayanan Mountvernon.org, adireshin yanar gizon kungiyar da ke kula da kadarorin shi. Babu wani bayani a game da murnar zagayowar maulidin haihuwar shi a Mount Vernon cikin bayanan da aka adana, yayin da kundin rubutun shi yayi nuni da cewa shi haziki ne a faggen aiki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG