A yau Talata, Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada aniyarsa ta Amurka za ta karbe iko da zirin Gaza tare da sakewa al'ummarsa matsuguni na dindindin, lokacin da ya gana da Sarki Abdalluh na Jordan a daidai lokacin da adawa da shirin ke kara fadada a tsakanin Larabawa kawayen Washington, ciki har da kasar Jordan.
Shugaban na Amurka ya nuna alamar cewa ba zai sauya matsaya ba game da shirin Amurka na karbe iko da Gaza tare da debe firgitattun mazauna cikinta da kuma sauya yankin da yaki ya daidaita.
"Za mu karbe ta. Zamu tallafe ta, nuna mata kauna. A karshe zamu farfado da ita, inda zamu kirkiri dimbin guraben aikin yi ga al'ummar gabas ta tsakiya," kamar yadda Trump ya bayyana game da Gaza. inda yace shirinsa zai samar da zaman lafiya a yankin.
Trump yace zai duba yiyuwar hana tallafin da Amurka ke baiwa Jordan matukar taki yarda ta sake tsugunar da Falasdinawa.
Tunda fari Sarki Abdallah yace ba zai amince da yunkurin kwace iko da yankin da tilastawa Falasdinawa barin wurin ba
"Manufa ita ce a aiwatar da shirin ta yadda za'a yiwa kowa adalci," a cewar sarkin, ba tare da fitowa karara ya bayyana goyon baya ko akasin hakan ga shirin na Trump ba.
Dandalin Mu Tattauna