A daidai lokacin da masu ba shi shawara akan kasuwanci ke kammala shirye shiryen daukar matakan ramuwar gayya kan duk wata kasa da ta caji kudaden haraji kan kayan da ake shiga da su daga Amurka, shugaba Donald Trump ya bayyana a jiya Laraba cewa, zai matsa wajen ganin an rage kudin ruwa, hadi da manufofin shi na haraji.
Shugaba Trump ya fada ta kafar sada zumuntar zamani a jiya Laraba cewa, yakama kudin ruwa da ake karba ya yi kasa, wani abu da zai tafi kafada kafada da karin harajin dake tafe. Lokaci ne da Amurka zata barje gumin ta inji Trump.
Domin ganin dorewar samun cikakken cin gashin kan baitilmalin kasa daga siyasa, bisa al’ada shugabannin Amurka kan kaucewa tsalma baki kan abubuwan da suka shafi manufofi da suka shafi kudi, da jadawalin tsarin kudin ruwa, wanda alhaki ne na babban bankin kasa.
To sai dai duk da haka shugaba Trump bai janye kan shi daga hakan ba. A yayin wani yawabi da ya yi ta kafar video ga taron tattalin arzikin duniya a Davos na kasar Switzerland a watan Janairu, shugaba Trump yace, zai nemi da a hanzarta sauko da kudaden ruwa.
Dandalin Mu Tattauna