Hukumar kashe gobarar Nome tace “matukin jirgin ya shaidawa hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewar yana niyar sanya jirgin a tsarin jira yayin da yake jiran titin saukar jiragen ya zama babu komai akai” gabanin bacewarsa.
A yau Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Isra’ila zata mikawa kasarsa iko da Gaza bayan lafawar rikici tare da tsugunar da al’ummar zirin a wani wuri na daban, abinda yace ba zai bukaci tura dakarun sojin Amurka zuwa yankin ba.
Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.
An dauki matakin ne domin nuna adawa da abin da sakataren ma'aikatan fadar White House Will Scharf ya bayyana da dabi'un kyamar Amurka a hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Trump ya ayyana Gaza da “wurin da aka rusa” sannan ya kwatanta batun da sama wa mazauna zirrin Gaza da wani matsuguni a madadin inda suke da yaki ya daidaita.
'Muna kokarin ganin cewa mun yi sulhu don kawo karshen yake yaken da ake yi, ko kuma a kalla a ce mun taimaka don ganin sun yi sulhu tsakaninsu. Amma babu taimakon da ake bamu. Wannan shine babbar manufar MDD.'
A ranar Litinin ne aka dakatar da ayyuka a Hukumar Tallafawa Kasashe masu tasowa ta Amurka ta USAID mai gudanar da ayyukan tallafi na biliyoyin dala ga kasashen waje.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, akwai yuwuwar Amurka ta cigaba da tallafawa Ukraine ta yin musanya da albarkatun karkashin kasar ta Ukraine.
Tunda fari Shugaba Claudia Sheinbaum ta sanar da amincewa da dakatar da fara kakaba haraji akan kayayyakin Mexico tsawon wata guda, bayan tattaunawa da Donald Trump.
Hakan na zuwa ne bayan da Musk, wanda ke jagorantar aikin yiwa tsarin gwamnatin tarayyar Amurka garanbawul (DOGE) ya bayyana da safiyar yau Litinin cewa ya zanta da Trump kan hukumar raya kasashen ta Amurka mai shekaru 60 kuma ya amince mu rufeta.”
Marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, manomin gaydar da ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan rikicin Watergate da yakin Vietnam ya mutu a watan Disamban 2024 yana da shekaru 100 a duniya.
Domin Kari
No media source currently available