Shugabannin Republican da na Democrat a kwamitocin kasafin kudi guda biyu a Majalisa sun gudanar da tattaunawa kan kudirin kashe kudin gwamnati a karshen watan Janairu, hadimai sun ce bangarorin biyu sun kuduri aniyar cimma matsaya. Sai dai fatan alheri yana dushewa a 'yan kwanakin nan.
Kasuwannin hannayen jari a Amurka sun yi kasa a ranar Juma'a yayin da ake nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyaki da haraji, yayin da wani rahoto da aka sa ido sosai akai ya ba da mabanbancin ma’ana game da kasuwar aikin yi a Amurka.
Masu aikin ceto a jihar Alaska sun ci gaba da bincike ya zuwa ranar Juma’a na wani jirgin sama da ya bace a ranar Alhamis da mutane 10 a ciki, da suka hada da fasinjoji 9 da matuki guda.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Jranar cewa ya kamata a kalli shirinsa na neman mallakar Zirin Gaza, a matsayin mai hada hadar gine-ginen gidaje, inda kasar zata zuba jari a wani bangare na duniya amma bata bada lokacin gudanar da aikin ba, yana mai cewa bama gaggawa a kai.
Hukumar kashe gobarar Nome tace “matukin jirgin ya shaidawa hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewar yana niyar sanya jirgin a tsarin jira yayin da yake jiran titin saukar jiragen ya zama babu komai akai” gabanin bacewarsa.
A yau Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Isra’ila zata mikawa kasarsa iko da Gaza bayan lafawar rikici tare da tsugunar da al’ummar zirin a wani wuri na daban, abinda yace ba zai bukaci tura dakarun sojin Amurka zuwa yankin ba.
Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.
An dauki matakin ne domin nuna adawa da abin da sakataren ma'aikatan fadar White House Will Scharf ya bayyana da dabi'un kyamar Amurka a hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Trump ya ayyana Gaza da “wurin da aka rusa” sannan ya kwatanta batun da sama wa mazauna zirrin Gaza da wani matsuguni a madadin inda suke da yaki ya daidaita.
'Muna kokarin ganin cewa mun yi sulhu don kawo karshen yake yaken da ake yi, ko kuma a kalla a ce mun taimaka don ganin sun yi sulhu tsakaninsu. Amma babu taimakon da ake bamu. Wannan shine babbar manufar MDD.'
A ranar Litinin ne aka dakatar da ayyuka a Hukumar Tallafawa Kasashe masu tasowa ta Amurka ta USAID mai gudanar da ayyukan tallafi na biliyoyin dala ga kasashen waje.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, akwai yuwuwar Amurka ta cigaba da tallafawa Ukraine ta yin musanya da albarkatun karkashin kasar ta Ukraine.
Domin Kari
No media source currently available