Yiwuwar janye tallafin Amurka a duniya na janyo muhawara a ciki da wajen kasar
Yayin da duniya ke ci gaba da fama da rikice rikice, wasu masu ruwa da tsaki na fatan manufofin Amurka karkashin Trump, na rage daukar matakan soji, zai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali
Jami’an Amurka sun bayyana cewar zai yi wuya a samu sauran mai rai bayan da wani karamin jirgin saman fasinja dauke da mutane 64 yayi karo da wani shelkwaftan soja a sarari samaniya tare da rikitowa cikin ruwan kogin Potomac na birnin Washington da ya fara kankarewa.
Ma’aikatan ba da agaji 300 ke cikin aikin ceton-da aka gudanar da galibinsa cikin tsananin duhu da sanyi.
Bayan jirgin saman farar hula mai dauke da fasinjoji 64 da kuma jirgin sama mai saukar ungulu na soji sun yi karo a sararin sama sun fado, ana fargabar cewa rayuka sun salwanta.
An shiga cece kuce bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa wajen kawo karshen zama dan kasa ta wajen haihuwa.
Sabon Sakataren Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka zai tabbatar da tasirin Amurka don ta maye gurbin China ta hanyar tabbatar da zaman lafiya a kudu maso gabashi da gabashin Asiya.
Kamfanin Tiktok na fuskantar wata dokar Amurka da ta umarce shi ya raba gari da mamallakinsa na kasar China Bytedance ko kuma a haramta shi a Amurka.
A ranar Litinin Gwamnatin Donald Trump ta kori lauyoyin ma’aikatar shari’a sama da 10 da suka gabatar da laifuffuka biyu a kan shi, cewar wani jami’i, a daidai lokacin da Republican ke hanzarta tabbatar da ikon ta akan ma’aikatar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi shelar labta wasu nau’ukan haraji, da tsauraran matakan VISA, da kuma sauran wasu matakai na ramuwar gayya kan kasar Colombia, bayan da ta ki yadda wasu jiragen sojin Amurka biyu, dauke da bakin haure, su sauka a kasar.
Sojojin 4 mata na Isra'ila sun yi murmushi, tare da daga hannu da babban yatsa ga dimbin jama'ar da suka tattaru a wani dandalin Falasdinu a birnin Gaza. Hukumar gidan yarin Isra'ila ta sanar da cewa ta kammala sakin Falasdinawa 200.
Amma ruwan sama kama da bakin kwarya a kan gaɓar tsaunuka da suka kone, na iya kawo barazanar sabbin matsaloli kamar malalowar toka mai guba.
Domin Kari
No media source currently available