Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kori Babban Jami’in Sa Idanu Kan Gudanarwar Hukumar USAID


Sallamar Paul Martin na zuwa ne kwana guda bayan da ofishinsa ya fitar da wani rahoto da ya caccaki yadda gwamnatin Trump ke kokarin wargaza hukumar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami babban jami’in dake sa idanu a kan yadda ake gudanarwa da tasrifi da kudade a hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID), kamar yadda kafafen yada labaran Amurka suka bada rahoto a yau Laraba.

Sallamar Paul Martin na zuwa ne kwana guda bayan da ofishinsa ya fitar da wani rahoto da ya caccaki yadda gwamnatin Trump ke kokarin wargaza hukumar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai AP da jaridar Washington Post da tashar talabijin ta CNN da wasu kafofin suka ba da rahoto.

Kafafen yada labaran sun ruwaito wata wasikar emel mai dauke da jumloli 2 da aka aikewa Martin daga fadar White House wacce ke shaida masa cewar an sallame shi daga kan mukaminsa, nan take,” ba tare da bayyana dalilan da suka sanya daukar matakin ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG