Jiya Alhamis Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dau matakan da ka iya kasancewa mafiya tasiri masu alaka da kasuwanci a matakin kasa da kasa tun a farkon wa’adin mulkin shi na biyun nan.
Trump, wanda ya rattaba hannu akan wani umarnin zartaswa da ya bukaci daukar matakan lafta harajin da suka kamaci matakan da aka dauka kan Amurka, ya gaya ma wani gungun ‘yan jarida a zauren Oval office, na fadarsa cewa, “wanda ya sarrafa kayayakinsa a Amurka ba zamu sanya wa kayakinsa haraji ba.”
Manufar ita ce rage gibin da aka samu a kasafin kudin Amurka da aka kiyasta ya kusan dalar Amurka triliyan biyu.
Shugaban ya kara da cewa, wannan matakin ya yi wa kowa adalci. Kada wata kasa ta yi korafi.”
Trump ya umarci wanda ya zaba a matsayin wanda ya ke so ya yi aiki da shi a matsayin Sakataren Harkokin Kasuwanci, Howard Lutnick, da wanda ya ke so ya yi wa mukamin wakilin kasuwanci ,Jamieson Greer, da su jagoranci tawagar jami’an da za su lissafa sabbin harajin da kuma lafta ma kayakin da abokan cinakayyar Amurkar ke shigar da su kasar.
Dandalin Mu Tattauna