Jirgin saman da ya daukesu ya tashi ne daga garin San Diego, na jihar California, inda ya sauka a wani sansani dake kusa da tashar jiragen saman kasa da kasa ta Juan Santamaria.
Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Junior ya ce babu wata hujja da za ta sa Amurka ta amince da zargin da ake ma Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID cewa ita ke tallafa wa Kungiyar Boko Haram
An fara murza gashin baki tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Zelenskyy kan makomar yakin Ukraine.
Majalisar Dattawa ta dauki haramar yin bincike kan zargin da dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi cewa Hukumar Gwamnatin Amurka mai Tallafa wa Kasashen Duniya, USAID, ita ce ta rika tallafa wa Kungiyar Boko Haram a Najeriya.
A baya-bayan nan ya sha alwashin dora harajin kaso 10 cikin 100 a dukkanin kayayyakin da ake shigarwa Amurka daga China, sannan kaso 25 akan kayayyakin karafa da gorar ruwa da aka shigo da su.
Babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Marco Rubio, na ci gaba da fadi tashin cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa a Ukraine da Gabas Ta Tsakiya
Shugaban Amurka Donald Trump yace akwai yiyuwar ganawa da Vladimir Putin “nan bada jimawa ba”, inda yace yana da yakinin cewar da gaske takwaran nasa na Rasha na nufin kawo karshen yakin Ukraine.
Babu wani bayani a game da murnar zagayowar maulidin haihuwar shi a Mount Vernon cikin bayanan da aka adana, yayin da kundin rubutun shi ya yi nuni da cewa shi haziki ne a faggen aiki.
Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya yi kashedi ga kawayensu na Turai da suke halaratan taro kan tsaro a Munich na kasar Jamaus game da barazanar cikin gida.
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke samar da kudade ga kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki harda boko haram.
Domin Kari
No media source currently available