Jiya Talata ne wata dusar kankara ta fara zuba a fadin jihohin Atlantic na tsakiya, wanda yayi sanadin hadaruka da dama akan titunan da suka yi santsi a dalilin kankara, lamarin da ya sa aka rufe makarantu da kuma fargabar yiwuwar fuskantar matsalar katsewar lantarki.
Dusar kankarar mafi yawa da ake hasashe ta sauka zata kai centimita 25, wanda ake hasashen zai kasance a wani yankin arewaci da tsakiyar jihar Virginia da gabashin yammacin Virginia.
Cibiyar kasa mai kula da al’amuran yanayi ta ce yawan kanƙarar da zuba a Kentucky zuwa yammacin Virginia tana iya kaiwa santimita 1.3 a wasu wurare da kwarin Roanoke dake yankin kudu maso yammacin Virginia.
Anyi hasashen za a fuskanci matsalar katsewar lantarki da yiwuwar bishiyoyi suyi barna a wuraren da kankara ke taruwa sossai.
An ci gaba da yin gargadin saukar dusar kankarar zuwa jiya Talata daga Kentucky zuwa kudancin New Jersey.
A wani bangaren kuma, wata kankarar da ake hasashen zata sauka da yawa a wani yankin da ya kama daga Kansas zuwa Great Lakes zata fara sauka da daren Talata kamar yadda cibiyar yanayin ta fada.
Dandalin Mu Tattauna