A jiya Laraba Amurka ta shawarci 'yan kasarta da su yi kaffa kaffa da wani sanannen masallaci a Islamabad, babban birnin kasar Pakistan, saboda barazanar ta’addanci.
Ofishin jakadancin Amurka a birnin Islamabad ne ya fitar da gargadin barazanar biyo bayan bayyanar wani faifan bidiyo a kafar sadarwar zamani a farkon makon nan, da ya rika nuna ayyukan wasu mayaka a masallacin Faisal na birnin, wani babban wurin zuwan 'yan yawon bude ido.
Dan takaitaccen faifan bidiyon ya nuna wani mutum dauke da tutar kungiyar Tehrik-i-Taliban’’ TTP, wadda Amurka ta ayyana da kungiyar ta’addanci a duniya.
An yada bidiyon a ranar Litinin ta kafar sada zumuntar zamani dake da alaka da kungiyar ta TTP. Ofishin jakadancin na Amurka ya haramta wa ma’aikatan shi zuwa masallacin har sai abin da hali yayi. An kuma shawarci Amurkawa da su kiyayi zuwa yankin, cewa, mayakan TTP fa sun fitar da barazana akan masallacin Faisal dake birnin Islamabad.
Dandalin Mu Tattauna