Hukumar CISA tace, a yanzu ya zama tilas ga kasashen dake son yin katsalandan ga zaben Amurka na ranar Talatan nan, su koma dogara da fayafayan bidiyon karya, da wasu kafafen yada labaran karya, domin kuwa ba yadda za su iya kutsawa ga gurbata sahihin sakamakon zaben.
Tuni dai Amurkawa kimanin miliyan 77 sun riga sun kada kuri’a tun da wuri yayin da Harris da Trump suke kokarin jawo karin miliyoyin magoya kafin zaben na Talata.
Manoman kasar Amurka za na shirin tafiya rumfunan zabe a ranar 5 ga watan Nuwamba domin zaben wanda su ke fatar zai kawo karshen matsin tattalin arziki da ke ci musu tuwo a kwarya.
Batun bakin haure ya kasance batu mai mahimmanci a zaben shugaban kasar Amurka na 2024, inda kaso 28% na Amurkawa suka bayyana shi a matsayin babbar matsala a kasar.
Jihar Georgia ta rika nuna alamun sake zaben tsohon shugaban Amurka Donald Trump a farko farkon yakin neman zaben shugabancin Amurka a shekarar 2024, lokacin da shugaba Joe Biden ke bisa takarar, kafin zuwan Harris.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna Harris, ‘yar takarar jam’iyyar Democrat da kuma Donald Trump na jam’iyyar Republican, sun yi kunnen doki a jihohin biyu.
Harris ta fadawa manema labarai cewa, “zan wakilci dukkan Amurkawa, har da wadanda ba za su zabe ni ba.”
Sanye da rigar kare lafiya mai launin lemo da rawaya Trump ya fada cikin shagube cewa shigarsa cikin motar sharar mataki ne "na girmama Kamala Harris da Joe Biden."
Dukkan ‘yan takarar biyu, na nuna rashin amincewa da junansu inda suke nuna daya bai cancanci ya jagoranci kasar na wa’adin mulki na shekaru hudu ba.
Jami’ai sun ce babu wanda ya jikkata, amma dai wasu daga cikin akwatunan tattara kuri’un sun lalace.
'Yan takarar biyu sun zafafa yakin neman zabensu yayin da ya rage 'yan kwanaki a garzaya rumfunan zaben a ranar Talata don zabar wanda zai gaji Shugaba Joe Biden.
Sannan masana sun ce bakin haure sabbin zama 'yan kasa da suka cancanci kada kuri’a zasu iya sauya akalar sakamakon zaben shugaban kasar da za ayi nan da 'yan kwanaki a watan Nuwamba, musamman ma a manyan jihohin raba gardama.
Domin Kari
No media source currently available