Perry ya yi wannan ikrari ne yayin zaman sauraron rahoton kwamitin majalisar a kan yadda hukumomin gwamnatin Amurka ke aiwatar da ayyuka da sarrafa kudade a jiya Alhamis.
Zaman mai taken “yaki da barna: Kawar Da Annobar Almundahana Da Zamba,” ya maida hankali ne a kan zargin barnatar da kudaden masu biyan haraji.
“Waye ke samun wani banagare na kudaden? ko wani a dakin nan ya kiyaye wadannan sunaye? saboda kudadenku, dala miliyan 697 a duk shekara, baya ga aika karin kudade ga Madrasas da ISIS da Al-Qa’ida da Boko Haram da ISIS Khorasan da sansanonin horas da ‘yan ta’adda. Wadannan su ne abubuwan da take daukar nauyi,” kamar yadda Perry ya bayyana.
Shafin yanar gizon kwamitin ya bayyana cewar zai yi aiki tare da ma’aikatar bin diddigin ayyukan hukumomin gwamnatin Shugaba Trump domin magance barna, da dakile almundahana tare da gudanar da cikakken bincike a kan yadda aka zambaci masu biyan harajin Amurka.”
Dandalin Mu Tattauna