Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Ya Bukaci Turai Ta Ba Jami'iyyun 'Yan Maza Jiya Dama A Dama Da Su


Mataimakin shugaban Amurka, J.D. Vance
Mataimakin shugaban Amurka, J.D. Vance

Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya yi kashedi ga kawayensu na Turai da suke halaratan taro kan tsaro a Munich na kasar Jamaus game da barazanar cikin gida.

Mataimakin shugaban kasar ya yi da cewa gwamnatocin Turai suna aiwatar da tsauraran matakan tantance bayanai kuma sun gaza daukar matakan da suka dace, har batun bakin haure ya wuce gona da iri.

"Barazanar da na fi damuwa da ita game da Turai ba ita ce Rasha, ko China ba, ko kuma wani dan kasar waje ba," yana fada a jiya Jumma'a. "Abin da na damu da shi shine barazana daga cikin gida, da yanda Turai ta kauce daga wasu muhimman dabi'unta, da kuma dabi'un da ta yi tarayyi da Amurka."

Vance ya yi Allah wadai da kasar Romania, kawar NATO, game da soke sakamakon zaben shugaban kasa a kan wata shaidar karya ta Rasha.

Ya ce "Idan zaku iya lalata dimokaradiyar ku saboda wasu tallace-tallacen yanar gizo na wasu ‘yan dubban daloli daga wata kasar waje, to, dimokaradiyar bata da karfi ma bare a farata,” in ji shi. "Zan bukaci abokaina na Turai da su zama masu hangen nesa."

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga jam'iyyu masu bin akidar mazan jiya masu adawa da bakin haure da ake hana su kafa gwamnatoci a Turai, ciki har da jam'iyyar Alternative for Germany (AfD).

“Dimokradiyya tana dogara ne kan akidar mutunta ‘yancin fadar albarkacin baki. Batun wariya bashi da gurbi a dimokaradiya, "Vance yana fada, yayin da yake nuni da "tattaunawar" Berlin a kan yunkurin yaki da tsattsauran ra'ayi a cikin kasar da har yanzu rawar da jam'iyyar Nazi ta taka a baya take addabarta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG