A jiya Lahadi, Shugaban Amurka Donald Trump yace akwai yiyuwar ganawa da Vladimir Putin “nan bada jimawa ba”, inda yace yana da yakinin cewar da gaske takwaran nasa na Rasha na nufin kawo karshen yakin Ukraine.
“Ba’a tsayar da lokaci ba tukunna, amma zai iya kasancewa nan bada jimawa ba,” kamar yadda Trump ya bayyana wa manema labarai, sa’o’i bayan da sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya yi kokarin rage kaifin hasashen da ake dashi game da muhimmiyar tattaunawar da ake shirin yi a birnin Riyadh akan kawo karshen yakin.
A dai dai lokacin da Rubio ke shirin jagorantar wata tawagar Amurka mai karfi zuwa tattaunawar da za’a yi da jami’an Rasha a babban birnin Saudiyya nan da kwanaki masu zuwa, iskar diflomasiya na ci gaba da kadawa yayin da kazamin yin Ukraine ke shirin shiga shekara ta 3 da farawa.
A jawabinsa ga manema labarai bayan saukarsa daga jirgin saman Shugaban Amurka, Trump yace tawagarsa na yin wata tattaunawa mai tsawo da wahalar gaske tsakaninta da jami’an Rasha, ciki har da jakadansa a gabas ta tsakiya Steve Witkoff wanda shugaban yace ya yi ganawar kimanin sa’o’i 3 da Putin a baya-bayan nan.
Dandalin Mu Tattauna