Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Legas Ta Gano Gidaje 86 A Karkashin Gada Inda Ake Biyan Kudin Hayar Naira Dubu 250


Gidaje da aka gano a karkashin gada
Gidaje da aka gano a karkashin gada

Kwamishin Muhalli da Albarkatun Ruwa na Legas, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta gano gidaje 86 a karkashin gadar Dolphin Estate, dake yankin Ikoyi, inda ‘yan haya kan biya Naira dubu 250 a matsayin kudin haya.

A wani faifan bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X, Tokunbo Wahab yace an yanyanka dakuna mai fadin kafa 10x10 da 12x 10.

Ya kara da cewar kwamitin Ko Ta Kwana Na Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar Legas yayi nasarar share ilahirin gine-ginen, ciki harda wata kwantena da ake gudanar da ayyukan laifi daban-daban a cikinta, daga karkashin gadar rukunin gidajen na Dolphin.

A yayin da yake rarraba faifan bidiyon, kwamishinan ya wallafa cewar, “askarawan tabbatar da tsaftar muhalli na jihar Legas sun kama wasu mutane 18 dake rayuwa a karkashin gadar rukunin gidajen na Dolphin a ranar 30 ga watan Afrilun daya gabata”.

“An bankado dakuna 86 masu fadin kafa 10x10 da 12x10 da kuma wata kwantena da ake amfani da ita wajen aikata laifuffuka da dama a karkashin gadar ta Dolphin Estate”.

“Askarawan Tabbatar da Tsaftar Muhalli na Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa na Gwamnatin Jihar sun ruguje gine-ginen”.

Haka kuma kwamishinan ya tabbatar da cewar ana biyan akalla naira dubu 250 a matsayin kudin hayar shekara a dakunan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG