Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laifin Wulakanta Naira: Cubana Ya Nemi Sasantawa Da Hukumar EFCC A Wajen Kotu


Pascal Okechukwu wadda aka fi sani da Cubana Chief Priest
Pascal Okechukwu wadda aka fi sani da Cubana Chief Priest

Lauyan Cubana Chief Priest ya shaidawa kotun cewar dukkanin bangarorin sun bukaci a sasanta takaddamar a bisa dacewa da tanade-tanaden sashe na 14(2) na dokar Hukumar EFCC.

Dan kasuwar nan mai suna, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da “Cubana Chief Priest” na duba yiyuwar sasantawa da Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati a wajen kotu game da tuhumar da take yi masa na wulakanta takardar kudin Naira a gaban Babbar Kotun Tarayya dake Legas.

Lauyan Cubana, Babban Lauyan Najeriya, Chikaosolu Ojukwu, ne ya shaidawa alkalin kotun, Mai Shari’a Kahinde Ogundare hakan a yayin zaman kotun na yau Alhamis.

Chikaosolu ya kara da cewar idan har Hukumar EFCC ta tabbatar da gaskiyar lamarin, toh akwai bukatar neman janye hujjojin kariyar da wanda ake kara ya gabatar domin sasantawa.

Lauyar EFCC, Bilkisu Buhari, ta tabbatar da batun lauyan wanda ake kara sannan ta shaidawa kotun cewar hukumarsu na cigaba da nazarin bukatar wadanda ake karar.

Sakamakon wannan tabbaci, lauyan wanda ake karar ya gabatarwa kotun bukatar neman janye hujjojin kariya kuma bangaren masu kara bai kalubalanci hakan ba don haka kotun ta amince da bukatar.

Daga bisani mai shari’a ogundare ya dage zaman kotun zuwa ranar 5 ga watan Yuni mai kamawa, domin bada rahoto akan sasantawar.

A ranar 17 ga watan Afrilun daya gabata, Hukumar EFCC ta gurfanar da Cubana Chief Priest a gaban kotu a bisa tuhume-tuhume 3 game da zargin yin watsi da sauya fasalin takardar naira a yayin wani biki a otel din Eko dake jihar Legas.

Ya ki amincewa ya amsa tuhumar da ake yi masa kuma an bada belinsa akan Naira miliyan 10 da kamilallun mutane 2 da zasu tsayawa masa akan naira milyan 10 kowannen su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG