Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGERIA: Gwamnan Ebonyi Ya Yi Karin Naira 10,000 Akan Albashin Ma'aikata


Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru

Gwamnan Jihar Ebonyi a Najeriya, Francis Nwifuru, ya sake bayar da karin Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar.

WASHINGTON, D. C. - Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta 2024 da aka gudanar a filin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki, babban birnin jihar.

Idan za a iya tunawa a watan Yulin 2023, bayan wata guda kawai a kan mulki, Gwamna Nwifuru ya kara Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar, inda ya ce zai ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata a jihar.

Gwamna Nwifuru, a cikin jawabinsa na bikin ranar ma’aikata ta 2024, ya jaddada cewa ma’aikatan gwamnati sun ci gaba da kasancewa abokan aikinsu.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da dorewa da zurfafa yanayin aiki na sada zumunta da hadin kan masana’antu, da nufin kara samar da ayyukan yi musamman da inganta shugabanci nagari.

Karin Naira 10,000 zai sa ma’aikatan jihar Ebonyi samun karin Naira 20,000 a kasa da shekara guda na gwamnatin Nwifuru.

A halin da ake ciki, wani jawabi da Farfesa Egwu Ogugua, shugaban kungiyar NLC na jihar ya karanta, ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da suke ciki, ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta kara daukar malamai a makarantun firamare da sakandare na gwamnati.

Sun kuma nuna godiya ga Gwamnan kan yadda ya kyautata ma ma’aikatan Ebonyi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG