Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Jinjina Wa Ma'aikatan Najeriya Yayin Bikin Ranar Ma'aikata


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Sakon sugaban na Najeriya yazo ne a wani sako da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar a ranar Litinin 1 ga Mayu, na bikin ranar ma’aikata, ta hanun mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Cif Ajuri Ngelale.

Shugaba Bola Tinubu ya taya ma’aikatan Najeriya murnar bikin ranar Mayu na wannan shekara ta 2024, inda ya yaba da rawar da suke takawa wajen ci gaban kasa.

Shugaban ya yaba da kwazon ma’aikatan, inda ya bayyana su a matsayin “jinin rayuwa” na kasar, inji Tinubu.

Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa ga yadda ma’aikatan Najeriya suka amince da zaman lafiya da ci gaban kasa, tare da sanin irin namijin kokarin da kishin kasa na daidaikun mutane a bangarori daban-daban.

Ya bayar da misalan ma’aikata a fagage daban-daban, inda ya yaba da irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.

“Daga jami’in da ke tabbatar da rubuta takardu da rarraba wasiku, jami’in tsaro wanda ya kasance mai aiki a kowane lokaci, malamin da ya tabbatar da makomar al’ummarmu ta hanyar ba da ilimi, likitan da ke aiki tukuru don ceton rayuka.

Daukacin ma’aikatan Najeriya wadanda suke cigaba da jajircewa don ganin cigaban al’amura,” in ji Shugaba Tinubu, yana mai yabawa da nuna jin dadinsa kan ci gaba da jajircewarsu.

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na inganta jin dadin daukacin ma’aikata, inda ya bayyana kokarin da ake yi kamar na bayar da albashi da kuma duba mafi karancin albashin ma’aikata. Ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yi imanin cewa, wadanda ke aiki wa kasa sun cancanci a biya su albashi mai tsoka da kuma inganta jin dadin jama’a, yana mai jaddada cewa,

“Ma’aikaci bai cancanci samun lada kawai ba, amma ya cancanci a ba shi albashi mai inganci,” inji shugaban.

Bugu da kari, shugaban kasar ya baiwa ma'aikatan Najeriya tabbacin sadaukarwar sa ba wai kawai inganta jin dadin su ba, har ma da inganta yanayin aikinsu da samar musu da kayan aikin da suka dace don samun nasara.

Sakon nasa ya jaddada kudurinsa na sauraron korafe-korafen ma’aikata da aiwatar da manufofin da ke taimakawa wajen kyautata rayuwarsu da samun nasara.

Shugaba Tinubu ya kammala sakon nasa da yi wa ma’aikatan Najeriya fatan alheri da murnar zagayowar ranar Mayu.

~Aminu Yusuf Aminu~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG