Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Jami’an Tsaro Da Su Dira Ma Dillalan Da Ke Boye Man Fetur


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Kwamitin kula da harkokin albarkatun man fetur na majalisar wakilan yayi kiran ga jami’an tsaro da su dira ma yan kasuwan da ke boye man fetur din suke kuma tsawwala farashin man yadda suka ga dama.

Yan majalisar wakilan sun zargi wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai da yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, inda su ka bukaci cibiyoyin tsaro da su taka musu birki.

Kwamitin kula da harkokin albarkatun man fetur na majalisar wakilan yayi kiran ga jami’an tsaro da su diram yan kasuwan da ke boye man fetur din suke kuma tsawwala farashin man yadda suka ga dama.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugabannin kwamitocin biyu, Ikenga Ugochinyere da Henry Okojie, 'yan Majalisar sun bayyana cewa, sun isar da sakonni ga masu ruwa da tsaki a harkar rarraban albarkatun mai da su kawo karshen dogayen layukan mai a fadin kasar.

Yan majalisar dokokin suka ce sun gana da wasu bangarori kamar su kamfanin mai na kasa, da hukumar kula da sa ido wajen rarraba man, da kungiyar dillalan mai ta kasa da kungiyar masu motocin dakon man ta kasa.

‘’Mun tattauna da su sosai, da zimmar gano musabbabin sake bullowar dogayen layukan mai a gidajen mai dake sassan kasar’’ a cewar wani bangare na sanarwar da aka fitar.

Sanarwar ta kara da cewa, daga abinda bincikensu ya gano, tabbas akwai wadataccen man fetur a kasa.

Majiya mai karfi ta tabbatar da cewa, lallai akwai wadataccen mai, akalla akwai kimanin lita bilyan daya da rabi na man fetur da zai iya kaiwa har kwanaki talatin.

To sai dai akwai takaici matuka ganin yadda dogayen layukan ababben hawa suka sake bayyana a gidajen mai, lamarin da aka danganta da matsalar sufuri na dakon man daga inda ake dauko shi.

Kwamitocin sun tabbatar da cewa, a yanzu an shawo kan matsalar kuma nan da yan kwanaki, matsalar karancin man zata zama tarihi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG