Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NAHCON Ta Fara Daukar Ma’aikatan Lafiya Na Aikin Hajjin Bana 


Shugaban NAHCON Ahmad Jalaal Arabi
Shugaban NAHCON Ahmad Jalaal Arabi

A ranar Laraba ne Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da fara daukar Ma’aikatan Kungiyar Likitoci ta kasa (NMT) zuwa aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin intanet na hukumar, inda aka sanar da cewa za a bude aikace-aikacen daga ranar 12 ga watan Fabrairu zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu da karfe 11.59 na dare inda za’a rufe.

A cewar hukumar, kwararrun da ake bukata a cikin 2024 NMT sune Likitoci, Likitocin Magunguna, Ma’aikatan jinya da Jami’an Lafiyar Muhalli kawai.

NAHCON ta ce "aikin kungiyar likitocin ta kasa a shekarar 2024 zai dogara ne da aikin sa kai daidai da ka'idar kasa da kasa kamar yadda Hukumar NAHCON ta amince."

Hukumar ta fayyace cewa babu wasu kudade na neman aiki, kuma cike fom din baya bada tabbacin zama memba a cikin 2024 NMT.

Likitoci da masu hada magunguna su kasance masu shekaru 28 zuwa 60, yayin da ma’aikatan jinya da sauransu su kasance masu shekaru 22 zuwa 60 don nemanzama membobin kungiyar.

Kunshe cikin sanarwar, hukumar ta cigaba da fayyace cewa "Masu neman izininzama memba na NMT: Dole ne su kasance ma’aikata ne a lokacin aikace-aikacen. Kuma dole ne ya kasance mutum bai yi aikin Hajji ba a cikin shekaru 3 da suka gabata (watau 2019, 2022 & 2023).

Sanarwar ta kara da cewa, "Dole ne ya shirya yin aiki na tsawon kwanaki 28 kuma mutum ya kasance a shirye ya ke ya ci gaba da zama a kasar Saudiyya har na tsawon kwanaki 45 kafin ya dawo Najeriya."

NAHCON ta ci gaba da cewa, duk mai neman wannan aiki dole ne ya aika da shaidar wani babba da zai tsaya masa a matsayin shaida, wanda wannan babban mutum dole ya kasance ko dai ma'aikacin gwamnati wanda bai kai matsayin GL 15 ba, basaraken gargajiya, Alkali ko shugaban karamar hukuma.

A karshe, gayyatar da NAHCON ta yi wa masu aikin sa kai, ya nuna irin muhimmiyar rawar da ma’aikatan lafiya ke takawa wajen kiyaye alhazai a lokacin aikin Hajjin 2024.

Hakan na nuni da irin rawar da za su taka na taimakawa wajen tabbatar da nasarar gudanar da aikin hajji mai cike da ruhi ga dukkan matafiya zuwa Saudiyya.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG