Shugaban Hukumar FCCPC, Babatunde Irukera, ya shaidawa Reuters cewar tarar tamkar wani umarnin kotu ne dake nuna amincewa da aikata laifi kwatankwacin yarjejeniyar amincewa da laifi domin samun maslaha a gaban kotu wanda ba iya daukaka kara akai.
Kasashen Najeriya, Mali, Tchadi da Nijar nan ake tunanin inda al’amura ka iya tabarbarewa sosai ganin dukkanninsu na fama da matsalar tsaro iri iri
Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin zakulo wadanda suka halaka mutane fiye da dari a karshen makon jiya, a jihar Filato.
‘Yan kabilar Kambari a Nigeria sun gudanar da babban taronsu na karshen shekara, tare da janyo hankalin ‘yan kabilar kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaunar juna.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajanta wa uwargidan Akeredolu, Betty, da kuma mukaddashin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, inda ya bukace su da su samu karfin gwiwa a wannan jarrabawa ta babban rashi da ta sami kasa baki daya.
Gwamna Akeredolu, mai shekaru 67, ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, an ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar jini mai suna “Leukemia”.
An gudanar da rantsuwar ne a dakin taro na Cocoa da ke ofishin gwamna da ke Akure, babban birnin jihar, wanda babban alkalin kotun, Mai shari’a Olusegun Odusola ya gudanar da shi da karfe 5:18 na yamma.
An haife shi ne a gidan Umar Na’Abba, babban dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958, marigayi Kakakin majalisar ya samu digirin farko a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1979.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibiti a Abuja ya na mai shekaru 65.
Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya da ya dade yana fama da ita, ya bar duniya yana da shekaru 67.
Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa, tare da hada karfi da karfe domin zakulo duk wadanda suka aikata wannan mummunan hari da tabbatar da kamo masu hannu a ciki.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.