“Gaskiya al’amarin yanzu fa sai ahankali, da muna biyan N500 daga Abuja zuwa Nasarawa amma yanzu kudin ya nunka zuwa N2000, wallahi muna wahala! In kazo da kaya ko mai kankantar su suma a ce sai ka biya kudin su.” inji Fidelis
Wannan kudiri da Majalidsar ta Wakilai ta sa a gaba ya sa masana tattalin arziki bayyana ra'ayoyin mabanbanta
Sai dai a wannan shekarar, lamarin ya sha banban da yadda aka saba saboda farashin man fetur ya ninninka kudinsa: hakan ya haddasa tsadar kudin mota ninkin-ba-ninkin.
"Ba ta yadda gwamnati za ta bari a yi irin wannan laifi ba ta hukunta wanda a ka samu da laifi ba." Ya ce.
Babban bankin ya ce yana gudanar da bincike bayan samun rahotannin da ke zargin bankunan kasar da hada kai da masu PoS wajen haifar da matsalar karancin naira, lamarin da ya ce yana shafar tattalin arzikin kasar.
Duk hukuncin da kotun ta yanke zai zama shi ne karshe kan wannan takaddama.
''Kudin mota damuwa ne; abinci damuwa ne; masara da muke saya dari da hamsin, dari biyu; dari uku; to yanzu na sayi masara da aka yi girbi Naira dari biyar, dari shidda; ka ga babu sauki’’, in ji Lami.
Yayin da Kotun Kolin Najeriya ta ce nan gaba kadan zatayi zaman sanar da hukuncin ta akan shari'ar kujerar gwamnan Kano, Rundunar 'Yan Sandan jihar ta nemi hadin kan kafofin yada labarai domin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a fadin jihar, gabani da kuma bayan sanar da hukuncin.
Komishinan Sufuri a jihar Filato, Davou Gyang Jatau yace gwamnati za ta farfado da dokar da zata tantance masu amfani da kekunan NAPEP da wadanda suka mallake su, ta hanyar amfani da na'urori na zamani.
Iyalan marigayi Alhaji Kabiru Muhammad daga jihar Naija sun ce har yanzu ba su ji komai ba dangane da batun biyan diyyar marigayin, wanda ya rasu a kasar Saudiyya, sanadiyyar makalewa a cikin na'urar da ke kai mutane gidan sama da ta lalace.
Daga gobe (Alhamis), ‘'yan Najeriya masu son yin bulaguro za su iya shiga motocin bas na gwamnati a bisa rangwamen kashi 50% na farashin da ake biya a halin yanzu da kuma na jiragen kasa kyauta.” Inji Alake
A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi ta Amurka (SEC) ta gurfanar da dan kasuwan nan na Najeriya Dozy Mmobuosi da wasu kamfanoni uku wanda shi ne shugabansu, inda ake zargin su da damfarar masu zuba jari.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.