Dubban matasan da suka mamaye babban titin da ke unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo, sun hana masu shiga birnin Kano domin kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.
'Yan majalisar dokokin jihar Bauchi sun zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa bayan da kotun daukaka kara ta tsige tsohon kakakin majalisar Abubakar Suleiman da mataimakinsa Jamilu Barade a ranar Laraba.
Al’ummomin kasashen Jamhoriyar Nijar da Najeriya na ci gaba da yin kiraye kirayen ganin an bude bodar kasar Nijar tare da janye takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Nijar bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar dokokin Najeriya takardar neman amincewarta domin ciwo bashin zunzurutun kudi dala biliyan 8.69 da kuma Fam miliyan 100.
Masu ruwa da tsaki a fannin Lafiya na Najeriya sun nanata muhimmancin kafa cibiyoyin ba da horo na musamman ga daliban da suka kammala karatun aikin likita a jami’o’in kasashen waje.
Rundunar sojan Najeriya ta yi Allah wadai da harin tsokana da wasu masu zanga-zangar siyasa su ka kai wa kwamban motocin sintirinta a kan hanyar Lafiya zuwa Makurdi.
Gwamnatin jihar Legas ta sake lalata baburan hawa guda 1,500 da jami’anta suka kwace daga hannun mutanen dake hawansu a kananan hukumomi guda 10 da yankuna 15 da aka haramta amfani da su.
A watan Yunin 2019, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara nada Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPCL.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 sai kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.
Rashin zaman lafiya na ci gaba da wanzuwa a wasu yankunan arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa tare da sakawa wasu al’umomi haraji na miliyoyin Naira.
Rundunar sojojin Najeriya ta kammala wani atisayen makwanni biyu da ta yi wa lakabi da “Operation Mugun Bugu” wanda shine na biyu a wannan shekara ta 2023.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.