Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Hon. Tajjudeen Abbass ya bayanna alhini game da rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilan Najeriya a Jamhuriya ta 8, marigayi Hon Ghali Umar Na’Abba wanda Allah ya yiwa rasuwa da sanyin safiyar yau Larabar 27 ga watan Disamba na 2023.
Dr. Tajudeen ya bayyana shi a matsayin "gogaggen dan siyasa wanda ya sadaukar da kansa ga yiwa Najeriya hidima kuma mai kishin kasa".
Ya ce a lokacin da Na’abba ya ke matsayin Kakakin Majalisa "ya tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a majalisar" inda ya jagoranci mambobin na wancan lokacin ga "daukan manyan matakai masu mahimmanci da suka kawo ci gaba ga dimokradiyya a Najeriya".
Cikin alhini, Dr. Abbass ya kuma tuna da yadda aka cimma nasarori da dama a zamanin shugabancin marigayi Na’abba a bangaren dokoki wadanda suka shimfidar da dimokradiyyar da Najeriya ta ke morewa a yau.
Dr. Abbas wanda shi ke rike da mukamin da marigayi Ghali Na’Abba ya rike a majalisar wakilan ya ce marigayin na daga cikin gogagun ‘yan majalisar da suka hidimtawa Najeriya a majalisar tarayyar kasar sannan ya karfafawa mambobin majalisar lokacin gwiwa a zamanin shugabancinsa a majalisar daban daban, misali ko shine nasarar da majalisar wakilai karkashin jagorancinsa ta samu wajen kasancewa na farko kuma daya tilo da ta kalubalanci wani yunkurin shugaban kasa wanda ta kai ga kafa Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).
Bayan karewar wa’adinsa a majalisar wakilan Najeriyar, marigayi Na’abba bai yi kasa a gwiwa ba inda "ya ci gaba da bada gudumawa a fagen demokradiyya, matakin da ya harzukamu, ya kuma bamu kwarin gwiwa", a cewar Kakakin Majalisa na yanzu, Dr. Abbass Tajudeen.
Ya ce, "Najeriya ta yi babban rashi", ya kuma mika "ta’aziyya ta ga ‘yan uwa da iyalan marigayi Alh. Ghali Umar Na’abba da wannan babban rashi da sukayi".
Ya kuma jajantawa gwamnatin Kano da wannan "babban rashin daya daga cikin ‘ya’yanta" sannan yayi addu’ar "Allah ya jikanshi da Rahama, ya kyautata makwancinsa ya kuma sa aljannatu Firdausi ta zama makomar sa".
Dandalin Mu Tattauna