Mataimakin shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce sun yi aiki tukuru, ba dare ba rana domin sun gano wurin da aka yi ta jita-jita cewa, an fifita yankin kudu kan yankin arewa a kasafin kudin 2024.
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince cewa kisan gillar da aka yi wa sama da mutane 100 a Filato, a jajibirin Kirsimeti ya faru ne sakamakon gazawar hukumar leken asiri da ta tsaro.
Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu ya ce hadin gwiwa da sauran matakan gwamnati abu ne mai mahimmancin gaske kuma dole in jinjinawa jagorancin jam'iyyarmu saboda dabbaka wadannan muradai masu mahimmanci.
Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya bayyana matukar damuwarsa a kan wasu hare-hare da aka kai a kauyukan jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 200, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.
Majalisar kasa na dab da kammala aiki kan kasafin kudin shekara 2024 kuma akwai gibi na ciwo bashi, yayin da masana tattalin arziki suka ba da shawarar cewa a sadaukar da basussukan da gwamnati ta ciwo wajen yi wa jama'ar kasar ayyuka.
Shugaban Hukumar FCCPC, Babatunde Irukera, ya shaidawa Reuters cewar tarar tamkar wani umarnin kotu ne dake nuna amincewa da aikata laifi kwatankwacin yarjejeniyar amincewa da laifi domin samun maslaha a gaban kotu wanda ba iya daukaka kara akai.
Kasashen Najeriya, Mali, Tchadi da Nijar nan ake tunanin inda al’amura ka iya tabarbarewa sosai ganin dukkanninsu na fama da matsalar tsaro iri iri
Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin zakulo wadanda suka halaka mutane fiye da dari a karshen makon jiya, a jihar Filato.
‘Yan kabilar Kambari a Nigeria sun gudanar da babban taronsu na karshen shekara, tare da janyo hankalin ‘yan kabilar kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaunar juna.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajanta wa uwargidan Akeredolu, Betty, da kuma mukaddashin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, inda ya bukace su da su samu karfin gwiwa a wannan jarrabawa ta babban rashi da ta sami kasa baki daya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.