‘’Akwai kayyayaki na yaki sosai kuma muna bada tabbaci ce wa za’a ga sakamako mai kyau. Kuma za’a rika tunkararsu duk inda su ke, duk dajin da suke a kai musu farmaki’’, in ji Matawalle.
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati.
Kwamitin Kudi a Majalisar Dokokin Kasa ya yi kira ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati masu samar da kudaden shiga su yi kokarin wuce abinda aka kawo a kundin kasafin kudin badi.
Gwamnan jihar Umar Muhammad Bago, ya bayar da wannan umurni ne a wani jawabi da ya gabatar a lokacin kaddamar da wani aikin noman shinkafa a jihar a ranar Lahadi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar kawo karshen fitinar da ta kaure a jihar Rivers tsakanin gwamnan Mista Fabura da magoya bayan tsohon maigidansa tsohon gwamna Nyelson Wike, wanda kuma shi ne ministan babban birnin tarayya.
Kungiyar 'yan Nijar mazauna kasashen waje reshen Najeriya da ake kira HCNE a takaice, ta yi kira ga shugabannin kungiyar raya tattalin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, da su janye takunkumin da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar.
Rundunar 'yan Sandan jihar Taraba ta yi nasarar kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan hakimin Sarkin Kudu da ke karamar hukumar Ibbi a jihar.
Shugaban Hukumar NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bitar matakan da hukumar ke dauka don tunkarar aikin hajin da ke tafe na shekarar 2024.
'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a wasu yankunan arewacin Najeriya duk da kalaman da mahukunta ke yi na cewa suna daukar matakai na magance matsaloin.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Oluremi Tinubu ta tarbi hudu daga cikin dalibai biyar na jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, da aka ceto kwanan nan daga hannun masu garkuwa da mutane.
Tun a watan Oktoba 'yan bindiga suka sace dalibai mata biyar a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumar Kididdiga Ta Kasa a Najeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da kasar ta ga hakan tun a shekarar 1996.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.