Jaridun cikin gida na Najeriya sun rawaito cewa, iyalai da manyan jami’an gwamnatin jihar Ondo sun tabbatar da rasuwar Gwamna Akeredolu a safiyar yau Laraba.
Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya da ya dade yana fama da ita, ya bar duniya yana da shekaru 67.
Gwamnan ya rasu ne sati biyu bayan mika ragamar mulki ga maitaimakinsa, kafin ya tafi kasar Jamus domin neman lafiya.
Rasuwar gwamanan ta kawo karshen fadi-tashi da cece-kuce da aka yi ta fama dashi na sarkakiyar mulki a jihar ta Ondo inda akwai lokacin da majalisar Jihar tayi yunkurin tsige mataimakinsa, amma daga bisani shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani aka sami dai-daito da kawo karshen rikicin.
Bayan shiga tsakani da shugaba Bola Tinubu ya yi, gwamnan ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, a ranar 13 ga watan Disamba, domin ya tafi jinya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnan ya mikawa mataimakinsa Aiyedatiwa ayyukan ofishin sa ba. A ranar 6 ga watan Yuni, Akeredolu ya mika mulki ga mataimakinsa ta wata wasika zuwa Majalisar dokokin jihar. A wancan lokacin, kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, ya bayyana cewa, hutun da ya fara a ranar 7 ga watan Yuni, an shirya tsawaita shi har zuwa ranar 6 ga Yuli, 2023.
Dawowar gwamnan Najeriya a ranar 7 ga Satumba, 2023, ya haifar da cece-kuce, musamman lokacin da ya zabi zama a Ibadan maimakon komawa Akure, babban birnin jihar kai tsaye. Jam’iyyar adawa ta PDP ta nuna shakku kan matakin nasa, yayin da hadiman gwamnan suka fayyace cewa ya ci gaba da zama a Ibadan ne domin samun lafiya da ci gaba da gyare-gyare a ofishinsa.
Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna damuwa kan yadda ake zargin wasu kwamishinonin sa da satar sa hannun gwamnan don amfanin kansu. Babban Lauyan Najeriya, Kayode Ajulo, da Kwamishinan Makamashi da Albarkatun Ma'adinai, Razaq Obe, sun bayyana wadannan ratanannin a matsayin zargi. Obe, a cikin wata wasika da ya aikewa mukaddashin gwamna Aiyedatiwa, ya bayyana hujjojin binciken da yake zato za su tabbatar da zargin.
Sai dai kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Misis Bamidele Ademola-Olateju, ta musanta wannan ikirarin, inda ta tabbatar da cewa, gwamnan yana da ikon sanya hannu a kan takardu. Sai dai ta zargi mukaddashin gwamnan da ta’azzara rikicin siyasa saboda wani buri na kashin kai.
Marigayi Gwamna Akeredolu dan jam'iyya mai mulki ne ta APC, ya ci zabensa na farko a watan Nuwamban shekara ta 2016, Akeredolu ya rike mukamai da dama kafin ya zama gwamna, daga cikin mukaman da ya rike a lokacin rayuwarsa akwai zama kwamishinan shari'a na jihar Ondo daga shekara ta 1997 zuwa 1999.
A shekarar 2008 marigatin ya taba rike shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya har na tsawon shekaru biyu.
Marigayi Gwamna Akeredolu ya rasu ya bar matar sa Betty da ‘ya’ya hudu.
Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67.
~Yusuf A. Yusuf~
Dandalin Mu Tattauna