Majalisar Dokokin Najeriya ta sake amincewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciwo wasu bashi da ya kai Dalar Amurka Biliyan 8.2, kwatankwacin Naira triliyan 7.5 domin lamuni na dogon zango.
Gwamnonin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya, karkashin shugabanta, kuma gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, sun sha alwashin dakile yawan kashe-kashen da ke afkuwa a yankin.
'Yan Najeriya na ci gaba da kalubalantar gwamnati akan matakan da take cewa tana dauka da zasu kawo karshen matsalolin tsaro, yayin da ake ci gaba da alhinin kisan kiyashi da aka yi wa jama'a a jihar Plateau.
Ministan Harkokin Cikin Gida Na Najeriya Olubunmi Tunji Ojo, ya bayyana cewa Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasfon yi da kanka a kasar, wanda hakan zai taimaka wajen rage wahalhalun da ‘yan kasar ke fama da su wajen mallakar fasfo.
Kungiyar 'yan boko ta Tijanniyya wato "International Tijjaniyya Burotherhood" ta bukaci 'yan Izala su bar 'ya'yan kungiyar su sakata su wala wajen yin wazifa a masallatan jami'o'i.
A wani yunkuri na tabbatar da tsarin kasafin kudi mai inganci, Shugaba Bola Tinubu ya umurci dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rika fitar da rahoto duk wata kan yadda suka aiwatar da kasafin kudin 2024.
A wani kakkausan martani da ta mayarwa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu game da jawabin sa na sabuwar shekara, jam’iyyar PDP ta bayyana shi a matsayin yaudara, da’awar karya, da alkawuran da baza’a iya cika su ba, inda ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kasa magance matsalolin da ke addabar al’umma.
Dan takaran Shugaban Kasa a karkashin tutar babbar jam’iyar adawa ta NDC a zaben 2024, kuma tsohon Shugaban Kasa, John Dramani Mahama, ya ba da tabbacin cewa, a shirye yake ya ba Musulman kasar karin hutun bukukuwan Idi, idan jam’iyarsa ta samu nasara a zabe mai zuwa.
Matasan yankin Sahel sun gudanar da taro da nufin tattauna a kan manyan kalubalen da suke cin karo dasu a wannan yanayi da kasashen uku dake yankin Sahel ke fama da matsalolin da suka dabaibaye su.
A wani martani mai ratsa zuciya da ya yi dangane da mummunar asarar rayuka da aka yi a jajibirin Kirsimeti a Najeriya, Fafaroma Francis ya mika addu’o’i da ta’aziyya ga iyalan da wani mummunan hari da aka kai jihar Filato ya rutsa da su.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.