Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Fitaccen Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Marigayi Ghali Umar Na'Abba


Tsohon Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba (Hoto: Instagram Ghali Na'abba)
Tsohon Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba (Hoto: Instagram Ghali Na'abba)

An haife shi ne a gidan Umar Na’Abba, babban dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958, marigayi Kakakin majalisar ya samu digirin farko a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1979.

Marigayi Ghali Umar Na'Abba wanda ya rike mukamin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta 4, ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba a wani asibitin Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

A lokacin rayuwar sa an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a shekarar 1999 daga jihar Kano, Na’Abba ya karbi mukamin shugaban majalisar ne watanni kadan bayan kaddamar da majalisar, bayan da kakakin majalisar na lokacin, Salisu Buhari daga jihar Kano ya yi murabus, a tsaka mai wuya na zargin takardar shaidar jabu.

An haife shi ne a gidan Umar Na’Abba, babban dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958, marigayi Kakakin majalisar ya samu digirin farko a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1979.

Ya yi makarantar firamare ta Jakara da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1969, sannan ya halarci Kwalejin Rumfa da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatu ta Afirka ta Yamma.

A tsakanin shekarar 1974 zuwa 1976, Na’Abba ya kuma halarci Makarantar share fage ta Kano, kafin ya samu gurbin shiga Jami’ar Ahmadu Bello a watan Oktoban 1976.

A shekarar 2004, ya kammala karatun digiri na biyu kan Jagoranci da shugabanci na gari a Makarantar Gwamnati ta Kennedy, a Jami'ar Harvard ta, Amurka.

Tun da farko Na'Abba ya kasance dan jam'iyyar PDP ne kuma ya wakilci mazabar Kano Municipal inda ya samu nasara a zaben watan Afrilun 1999.

Hawan sa zuwa mukamin shugaban majalisa na 8 ya biyo bayan rigingimun siyasa da aka yi na tsige shugaban jamhuriya ta hudu Salisu Buhari.

Abin da Na’Abba ya gada ya zarce harkar siyasarsa, wanda ya nuna irin dabi’un da mahaifinsa, Alhaji Umar Na'Abba ya tarbiyantar da shi kasancewarsa dan kasuwa, mai tsattsauran ra’ayi, kuma malamin addinin Musulunci.

Za a iya tunawa da irin gudunmawar da ya bayar a siyasar Najeriya yayin da al'ummar kasar ke juyayin rashin gogaggun 'yan siyasa. Allah ya jikan sa ya huta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG