Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koka da Rasuwar Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajanta wa uwargidan Akeredolu, Betty, da kuma mukaddashin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, inda ya bukace su da su samu karfin gwiwa a wannan jarrabawa ta babban rashi da ta sami kasa baki daya.
A cikin karramawar da ya yi, Shugaba Tinubu, ya nuna matukar alhininsa game da rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, inda ya bayyana shi a matsayin dan jiha mara tsoro kuma shugaba mai tausayi.
Shugaban ya bayyana Rotimi Akeredolu a matsayin fitacce kuma babban lauya, kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, in da ya yaba da irin namijin kokarin da ya yi wajen tsara tsaran shari’a a kasa. Muhimmin rawar da ya taka wajen kafa rundunar tsaro a yankin Kudu maso Yamma ya nuna aniyarsa ta magance matsalolin tsaro.
Shugaban ya jaddada aikin da Akeredolu ya gada a tsawon shekaru shida da yayi yana gwamnan jihar Ondo. Tasirin Akeredolu ya bayyana a fili a cikin manyan ci gaban ababen more rayuwa, wuraren ilimi, da ayyukan kiwon lafiya da aka samar a fadin jihar.
Karramawar ta jaddada irin jagoranci na musamman da Gwamnan ya yi a lokuta da suke cike da jarrabawa da wahala, kamar abin da ya faru, inda aka kashe mabiya cocin Katolika 40 na Owo a shekarar 2022.
A karshe, Shugaba Tinubu ya yi kira ga Mukaddashin Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya tabbatar da ya cigaba da aiwatar da manufofin alheri na mulkin da tsohon shugaban ya bari.
Dandalin Mu Tattauna