Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waiwaye Da Kokawa Game Da Rasuwar Gwamnan Jihar Ondo


Oluwarotimi Akeredolu
Oluwarotimi Akeredolu

Gwamna Akeredolu, mai shekaru 67, ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, an ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar jini mai suna “Leukemia”.

A wani yanayi na jimami da babban rashi, al’ummar jihar Ondo a Najeriya sun samu kansu a cikin kokawa da babban rashi na gwamna Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

Gwamna Akeredolu, mai shekaru 67, ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, an ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar jini mai suna “Leukemia”.

Gwamnan ya bar mata mai suna Betty Anyanwu-Akeredolu da ‘ya’ya hudu.

Rayuwarsa cike take da gwagwarmaya, fadi tashi, da abubuwan nazari musamman ga masu bibiyan al’amura na yau da kullum a fagen siyasa, harma da masu bibiyar tarihin siyasa a Najeriya.

Rashin lafiyar Gwamna Akeredolu ta haifar da cece-kuce a fagen siyasa a Najeriya, musamman a jihar ta Ondo, rahotanni sun nuna cewa likitocin fadar gwamnati ne ke kula da shi har zuwa rasuwarsa a jihar Legas.

Rashin lafiyar marigayin dai ya samo asali ne tun bayan dawowarsa daga hutun jinya na watanni uku a Jamus a watan Satumba. Duk da alamun farko na samun sauki, bukatar karin kulawar likita ya sa aka sake bashi hutu a ranar 13 ga Disamba, biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu.

An haifi gwamna Oluwarotimi Odunayo Akeredolu a ranar 21 ga watan Yuli, 1956 a garin Owo, mahaifinsa ya kasance mai wa’azi na addinin Kirista kuma sunan shi Reverend J. Ola Akeredolu.

Sunansa na tsakiya Odunayo yana nufin "Shekarar farin ciki" a harshen Yarbanci. Marigayin ya fara karatun firamare a garin Owo, Akeredolu ya ci gaba zuwa manyan makarantu irin su Kwalejin Aquinas da ke Akure da Kwalejin Loyola na Ibadan, da kuma makarantar “Comprehensive High School” da ke Ayetoro.

Hazakarsa ta neman ilimi ta kaishi har zuwa ga matakin digirin digirgir a fannin shari'a daga Jami'ar Ife a shekarar 1977.

Ya kasance Babban Lauyan Najeriya ne (SAN) wanda ya zama shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya a shekara ta 2008.

Bajintar sa ta fuskar shari’a ta kai ga kafa ma’aikatar lauyoyi na Olujinmi & Akeredolu, tare da Cif Akin Olujinmi, tsohon babban lauya kuma ministan shari’a na Najeriya. ya zama Gwamnan Jihar Ondo a ranar 24 ga Fabrairu, 2017.

A watan Nuwambar 2009, an tuhumi Akeredolu kan zargin cin hanci da rashawa, wanda ya gabatar da wata takardar koke da Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi na Uku, Sakataren Jin Dadin Jama'a, da Mataimakin Sakataren Kudi suka yada, mai taken "Korafe-korafen da kuke yi na yaudara da cin zarafin NBA."

Duk da wannan zargi, Majalisar Zartaswar Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta yi nazari tare da yin watsi da tuhumar da ake yi masa.

Da ya koma fagen siyasa, Akeredolu na daga cikin ‘yan takarar da ke neman zama dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam’iyyar ACN a zaben 2012.

A watan Yulin 2012, yayin taron jam’iyyar ACN a Akure, Akeredolu ya fito a matsayin dan takarar gwamna na ACN, wanda hakan ya sa aka fara fafatawa da mai ci Olusegun Mimiko da Olusola Oke na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Da yake yin alkawura a wancan lokacin, Akeredolu ya yi alkawarin samar da ayyuka 30,000 a cikin kwanaki 100 na farko a ofis, alƙawarin da ya sa ya gabatar da CV sama da 10,000 ga ofishin yakin neman zabensa.

Tafiyarsa ta siyasa ta kai kololuwa a shekarar 2016 lokacin da ya samu tikitin tsayawa takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo. A ranar 27 ga watan Nuwamba, 2016, ya samu nasara a zaben, inda ya samu kuri’u 244,842 inda ya doke Eyitayo Jegede na jam’iyyar PDP da Olusola Oke na jam’iyyar AD, a cewar Farfesa Ganiyu Ambali, jami’in zaben INEC.

Bayan haka, an rantsar da Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2017, a Akure.

A wani yunkuri na neman wa’adi na biyu, Akeredolu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a ranar 21 ga watan Yuli, 2020, kuma ya ci gaba da samun nasara a zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi a ranar 10 ga watan Oktoba, 2020, wanda ya doke Eyitayo Jegede na PDP, Agboola Ajayi na ZLP, da wasu 'yan takarar sauran jam'iyyu.

Akeredolu ya kasance a matsayin Shugaban Gwamnonin Kudu Maso Yamma, wanda hakan ya shaida irin tasirinsa a fagen siyasar yankin da kawo ayyukan sauyi. Daga cikin sauye-sauyen akwai kafa kungiyar tsaro ta Kudu-maso-Yamma, mai suna Amotekun, wadda ta yi fice sosai wajen kokarin tabbatar da tsaron yankin.

Wa'adin Gwamna Akeredolu na biyu bai rasa nasaba da kalubale ba. Damuwar rashin lafiya ce ta sa aka kwashe shi zuwa kasar waje a watan Yuni, inda ya dawo Najeriya a watan Satumba, amma ya ci gaba da zama a Ibadan, jihar Oyo, saboda rashin lafiyarsa ta tabarbare.

Jam’iyyun adawa da masu fafutuka sun matsa lamba kan ya yi murabus ko kuma ya mika mulki ga mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar, lamarin da ya sa shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani. Daga karshe gwamnan ya mika ragamar mulki ga Aiyedatiwa a farkon watan Disamba, inda ya fara hutun jinya zuwa Jamus.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Bamidele Ademola-Olateju, ya sanar da rasuwar gwamnan a hukumance. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta isar da labarin mai ban tausayi, "Mai girma gwamna ya bar duniya cikin lumana da sanyin safiyar yau Laraba 27 ga watan Disamba, 2023." An aika da wasika zuwa ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, inda aka sanar da shi rasuwar Akeredolu.

Oluwarotimi Akeredolu da Shugaban Kasa Bola Tinubu
Oluwarotimi Akeredolu da Shugaban Kasa Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koka da Rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu.

A cikin karramawar da ya yi, shugaba Bola Tinubu, ya nuna matukar alhininsa game da rasuwar gwamnan inda ya bayyana shi a matsayin dan jiha mara tsoro kuma shugaba mai tausayi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG