Shugaban Hukumar NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bitar matakan da hukumar ke dauka don tunkarar aikin hajin da ke tafe na shekarar 2024.
'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a wasu yankunan arewacin Najeriya duk da kalaman da mahukunta ke yi na cewa suna daukar matakai na magance matsaloin.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Oluremi Tinubu ta tarbi hudu daga cikin dalibai biyar na jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, da aka ceto kwanan nan daga hannun masu garkuwa da mutane.
Tun a watan Oktoba 'yan bindiga suka sace dalibai mata biyar a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumar Kididdiga Ta Kasa a Najeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da kasar ta ga hakan tun a shekarar 1996.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana alhininsa game da rasuwar babban ma’aikacin yada labarai, Kabiru Usman Fagge, wanda ya rasu ranar Juma’a a kasar Amurka.
Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayar da gudunmuwar kudi Naira miliyan 180 ga wadanda harin bam din ya rutsa da su a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Tsohon Ma'aikacin Sashen Hausa Alhaji, Kabiru Usman Fagge ya rasu a nan Amurka sakamakon rashin lafiya.
Dokta Chukwuemeka Ezeife, wanda jigo ne a kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ya rasu ne a babban asibitin Tarayya da ke Abuja a sakamakon rashin lafiya.
Hukumar yaki da sha ko tu'ammuli da miyagun kwayoyi a Najeriya ta hada hannu da sauran jami'an tsaro domin kara tsaftace al'umma daga illolin tu'ammuli da miyagun kwayoyi, yayin da shekara ta 2023 ke bankwana, bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara ke kara matsowa, .
Kwanaki 16 cir kafin a cika wa’adin da kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPCL ya sanya na fara aikin matatar man fetur na Fatakwal, masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur sun nuna shakku ga yiyuwar hakan ganin cewa ba’a ma fara aikin gwaji a matatar da ake sake ginawa din ba.
Mai ba shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan al’amurran siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya ce ba wani dalilin da zai sa shugaban kasar ya yi katsalandan ga lamuran shari'a wanda bangare ne mai cin gashin kan shi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.