Katafariyar matatar mai da hamshakin attajirin nan Aliko Dangote ya gina a Najeriya ta samu gangunan danyen man fetur na farko, wata gagarumar cigaba na aiki da ya sha fama da jinkiri da nufin biyan bukatun man kasar gaba daya, a cewar sanarwar kamfanin yau Asabar
Kwamitocin Kula da Harkokin Kudi da yadda ake kasafta su a Majalisar Dokokin Najeriya sun ce ba za su lamuncewa sakaci daga ma'aikatan hukumomin gwamnati ba, a yayin da suka zo kare kasafin kudinsu a gaban kwamitoci daban-daban na majalisar.
Shugaban Ma'aikata a fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, a wata sanarwa da ya wallafa a kafar sadarwa ta X (twitter) a hukumance, ya karyata labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo kan makudan kudaden da ake zargin an ware wa ofishinsa a kasafin kudi.
Ganin yadda adadin wadanda su ka rasu sanadiyyar harin bam na jirgin sojan Najeriya yake karuwa bayan rasuwar wasu masu jinya, hadakar kungiyoyin matasa a Arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa kan abin da ya faru a garin Tudun Biri na Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede, ya bayyana damuwarsa kan yadda matasan Najeriya ke tafka ta’asa wajen aikata laifuka ta yanar gizo.
Kungiyar masu fiton kayayyaki ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bude tashar kan iyaka ta Lolo da ke tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.
Masu sharhi da masana harkokin hakkin dan Adam na ganin ana samun karuwar take hakkokin bil’adama a Najeriya.
Mako guda bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki kasafin kudin badi, har yanzu wakar nuna goyon bayan Tinubu da aka rera a zauren Majalisar ta bata wa yan Najeriya rai, inda wasu ke ganin wannan mataki tamkar nuna wa Majalisar raini da kaskanci ne.
Ana kara samun karuwar mutanen da su ka rasu biyo bayan harin kuskure na jirgin sojan kasan Najeriya kan masu taron Mauludi a garin Tudun Biri na Karamar hukumar Igabin jihar Kaduna, yayin da 'yan-uwa da iyalan wadanda abin ya shafa suka ce wasu masu jinya a asibiti sun kara rasuwa a ranar Talata.
Al'ummomi mazauna yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro a Najeriya na ci gaba tsokaci tare da nuna mamakin cewa ashe gwamnatin kasar na da jiragen yaki da ke iya hallaka jama'a da yawa, amma ta bar su 'yan bindiga na cin zarafin su.
Wata babbar kotun jihar Yobe da ke garin Pataskum ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan jami'in sojan nan Lance Corporal John Gabriel da ya hallaka fitaccen malamin addinin musuluncin jihar, Sheikh Bagoni Aisami.
Kungiyoyi da daidaikun mutane na nuna juyayi da bukatar bin kadun ma'abota halartar Maulidi a yankin Igabi a jihar Kaduna da bom din rundunar sojan Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin 30 a cikin su.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.