“Shawarana shine gwamnati ta manta da manya manyan ayuka. Ta mayar da hankali wurin tsaro. Saboda in ka kaddamar da babban aiki amma babu tsaro, ba abunda ka yi. Tafiyar ma ya zama wahala”, a cewarsa.
Mabiya addinin na Kirista da Musulmi sun jaddada muhimmancin hadin kai da daina nuna wa addinan juna kyama da tsangwama don samun ci gaba da wanzarda zaman lafiya.
Lokacin sha, ya kamata a sha lemu ba giya ba. Ba lokaci ba ne da za’a sha a bugu ba, kuma ba lokaci ba ne da za a tada hankalin mutane.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Kirisotci a Jihar Borno, Ravaran Abraham Ogah ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da su yi bukukkuwan Kirsimeti cikin godiya da addu’a domin yin murnar zagayowar ranar haihuwar Isa Almasihu.
“Gwamnati ta ga al’amarin, kuma za ta binciki duk abin da ya faru, don tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.
“Gaskiya al’amarin yanzu fa sai ahankali, da muna biyan N500 daga Abuja zuwa Nasarawa amma yanzu kudin ya nunka zuwa N2000, wallahi muna wahala! In kazo da kaya ko mai kankantar su suma a ce sai ka biya kudin su.” inji Fidelis
Wannan kudiri da Majalidsar ta Wakilai ta sa a gaba ya sa masana tattalin arziki bayyana ra'ayoyin mabanbanta
Sai dai a wannan shekarar, lamarin ya sha banban da yadda aka saba saboda farashin man fetur ya ninninka kudinsa: hakan ya haddasa tsadar kudin mota ninkin-ba-ninkin.
"Ba ta yadda gwamnati za ta bari a yi irin wannan laifi ba ta hukunta wanda a ka samu da laifi ba." Ya ce.
Babban bankin ya ce yana gudanar da bincike bayan samun rahotannin da ke zargin bankunan kasar da hada kai da masu PoS wajen haifar da matsalar karancin naira, lamarin da ya ce yana shafar tattalin arzikin kasar.
Duk hukuncin da kotun ta yanke zai zama shi ne karshe kan wannan takaddama.
''Kudin mota damuwa ne; abinci damuwa ne; masara da muke saya dari da hamsin, dari biyu; dari uku; to yanzu na sayi masara da aka yi girbi Naira dari biyar, dari shidda; ka ga babu sauki’’, in ji Lami.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.