Sarkin Musulmin yace za a fara azumin watan Ramadana a Najeriya a gobe Asabar.
“Saka harajin ya zama wajibi, saboda kasashe da dama ba sa kyauta mana, ciki har da kawayenmu da abokan hamayyarmu.” In ji Trump.
Shugabannin ‘yan tawayen na zargin gwamnatin Congo da haddasa fashewar suna masu cewa wadanda suka kai harin na cikin wadanda suka mutu.
“Fiye da rabin al’ummar kasar – mutum miliyan 24.6 – na fuskantar yunwa mai tsanani. Ayyukan kiwon lafiya sun rushe gaba daya. Miliyoyin yara sun shiga rudani kuma an yanke su daga ilimi na hukuma.
Kungiyar kasashen AES da ta kunshi Mali, Nijar da Burkina Faso ta bayyana shirin tattaunawa da kungiyar ECOWAS dangane da yadda za su yi hulda irin ta kungiya da kungiya da nufin tabbatar da dorewar 'yancin walwala da zirga-zirgar al'umominsu a yankin yammacin Afirka baki daya
Haka kuma fadowar jirgin ta sabbaba daukewar wutar lantarki a unguwannin dake kusa da wurin tare da lalata gidaje da dama a yankin.
Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) sun nada tsaffin shugabannin Habasha da Kenya da Najeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a jamhuriyar Dimokiradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin kasar.
Likitoci marasa shinge sun dakatar da aiyukan su a yakin da fari ya yiwa katutu na sansanin Zamzam a Sudan sakamakon karuwar hare hare da rikici a yankin.
Tun bayan da ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani a karon farko ya kai ziyara a wasu kauyukan jihar Tilabery dake fama da ayyukan ‘yan ta’adda
Jami’ai sun ce sojojin Sudan a ranar Lahadi sun yi nasara a kawo karshen kawanya ta sama da shekara guda a kan muhimmin birnin Obeid, inda suka maido da hanyar shiga wani muhimmin yanki a kudu maso tsakiyar kasar.
Ana zargin rashin ruwa mai tsafta ne ya haddasa barkewar kwalara a birnin Kosti dake kudancin kasar bayan da injin bada ruwa na birnin ya daina aiki sakamakon harin da wata kungiyar sojojin sa kai ke yi, a cewar ma’aikatar kiwon lafiya.
Daruruwan jami'an 'yan sandan Congo da suka koma kungiyar ‘yan tawayen M23 sun rera waka da tafawa a birnin Bukavu da suka mamaye a jiya Asabar, suna shirin sake samun horo karkashin ikon ‘yan tawayen da suka bayyana niyyar zama a wurin da kuma gudanar da mulki.
Domin Kari
No media source currently available