A nan ya fara da mahakar zinaren kauyen Samira kafin ya isa kauyen Libiri inda a watan Disamban bara 'yan ta'adda suka halkaka mutane a kalla 20 tare da tilasta wa jama'a ficewa daga garin.
A wani jirgi mai saukar angulu na rundunar sojojin Nijar ne Janar Tiani ya isa wannan yanki dake gab da iyakar kasar da Burkina Faso.
Shugaban ya fara da sauka a kamfanin hakowa da tace zinare SML dake kauyen Samira mai tazarar km 140 a kudu maso yammacin birnin Yamai, mazaunin kamfanin mallakar gwamnatin Nijar da hadin gwiwar masu hannun jarin ketare na daga cikin wuraren da suka fi fama da matsalolin tsaro a jihar Tilabery.
A cewar mai sharhi kan sha’anin tsaro Abdourahamane Alkassoum ziyarar abu ne da ka iya karfafa gwiwa ga ma’aikatan kamfanin da ma al’ummar kauyen Samira.
Kauyen Libiri dake kusa da kauyen na Samira ya fuskanci wani kazamin harin ta’addanci a ranar 11 ga watan Disamban 2024 inda maharan suka hallaka farar hula 20 sannan suka cinna wa garin wuta, lamarin da ya sa jama’a arcewa.
To amma watanni 3 da faruwar wannan aika-aikar mutane sun fara komawa gida, mafari kenan da Janar Tiani ya yi amfani da wannan dama domin jajanta musu tare da basu tallafin cimaka sannan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta karfafa matakan tsaro.
Ya kuma karkare rangadinsa da sansanin soja mai lamba 313 dake ayyukan tsaro a wannan shiyya. Yana mai nuna gamsuwa da yadda aiki ke gudana tare da basu albishirin karfafa matakan da a karkashinsu za a girke wata bataliya ta musamman.
A ra’ayin kwararre kan sha’anin tsaro Abass Moumouni ziyarar abu ne da ka iya tasiri a wajen askarawan kasa da ma al’umomin da ke fama da matsalolin tsaro baki daya.
Wannan rangadi ko bayan kasancewarsa na farko da Janar Tiani ke kai wa a yankunan da al’umma ke fama da aika-aikar ‘yan ta’adda wasu na ganin abin a matsayin wata amsa ga masu yi masa zargi game da rashin zuwansa yankunan karkara domin gane wa kansa halin da talakawa ke ciki.
Saurari cikakken rahoto daga SouleyMoumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna