Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce za a yi tafiya da kowa a tattaunawar, wadda za ta tsara abubuwan da gwamnati za ta fi baiwa muhimmanci, sannan kuma za ta tsara jadawalin sauyin mulkin.
Fafatawar ta yau Talata na faruwa ne a kusa da garin Ihusi mai tazarar kilomita 70 daga babban birnin lardin Bukavu da kuma filin saukar jiragen saman yankin mai nisan kilomita 40.
Rikicin na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo yana kara muni ne bayan da kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kwace Goma, wani gari mai muhimmanci a lardin Kivu ta Arewa dake kudancin DR Congo.
Hukumomi sun ce sun kubutar da bakin haure 76 sannan sun tsare wani dan Libya da wasu ‘yan kasar waje 2 bisa tuhumar su da ake yi da tsarewa da kuma azabtar da bakin hauren.
Sam Nujoma, dan gwagwarmayar neman ‘yancin kai wanda ya jagoranci Namibia samun ‘yancin kai daga mulkin wariyar launin fata na Afrika ta Kudu a shekarar 1990, ya kuma yi shugaban kasar na tsawon shekaru 15 ya rasu. Yana da shekaru 95.
Jakadan jamhuriyar Benin a Nijar ya roki gafarar al'ummar jamhuriyar Nijar a madadin gwamnatin Patrice Talon da al'ummar kasar baki daya, dangane da sabanin da ya biyo bayan takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa a Nijar a shekerar 2023, a sanadiyar juyin mulkin da soja suka yi wa gwamantin farar hula.
Taron da shugabannin kasashen Afirka suka yi don magance rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a yau Asabar ya yi kira da a tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba, cikin kwanaki biyar.
Sama da mutane 50 ne aka kashe a kusa da garin Gao da ke arewa maso gabashin kasar Mali a ranar Juma’a, bayan da wasu mahara dauke da makamai suka yi wa ayarin motocinsu kwantan bauna tare da rakiyar sojojinsu, in ji wani jami’in yankin da mazauna yankin.
Yayin da Janhuriyar Nijar ke dada daukar tsauraran matakai kan harkokin shigi da fici, ta na kuma sassauta ma bakin da ke cikin kasar
A yau Alhamis Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar jihohi 2 a kudancin Sudan “na gab da afkawa cikin bala’i” bayan da rahotanni suka bayyana cewar barkewar sabon rikici a daya daga cikin biranensu ya hallaka akalla mutane 80.
Domin Kari
No media source currently available