M23 ta kara dannawa a makon da ya gabata zuwa cikin birnin mafi girma a gabashin Dimokaradiyar Jamhuriyar Congo wanda ya fuskanci fashi da tashin hankali yayin da sojojin Congo suka fice daga wurin ba tare da fada ba
Kungiyar M23 da ta kwace wurare da dama a gabashin Congo da muhimman albarkatun kasa, ta haddasa fargabar fadawa cikin babban yaki, lamarin da kuma ya kai Kwamitin Sulhun MDD ga amincewa da wani daftari na bai daya a ranar Juma’a da ya yi kira ga kawo karshen tashin hankali da kuma janyewar ‘yan tawayen daga yankin.
A birnin Bukavu, babu wata alama dake nuna wannan kira zata yi tasiri. ‘Yan sandan da aka tara su wuri guda kana suka sanya sabbin rigunan sarki da bakaken hula, an fada musu cewa za a kai su a basu horo kana su dawo su taimakawa ‘yan tawayen M23.
“Da fatan zaku je ku dawo mana lafiya saboda dukkan mu baki daya mu ci gaba da aikin ‘yantar da kasar mu,” in ji kwamandan ‘yan sanda Jackson Kamba.
Kimanin ‘yan sanda 1,800 ne suka mika wuya kuma za a tura su sake daukar horo, tare da wasu 500 da suke shirin yin haka, a cewar Lawrence Kanyuka, kakakin hadakar kungiyoyin ‘yan tawaye ta AFC da ta hada da M23.
A nan take gwamnatin Congo bata maida martani ga bukatar jin ta bakinta ba.
Dandalin Mu Tattauna