A yau Talata MDD tace akwai matukar damuwa dangane da yanayin bada agaji a garin Goma na Jamhuriyar Congo da aka yiwa kawanya, ganin yawan mutanen da aka raba da muhallansu, ga karancin abinci da satar kayan agaji da ambaliya ga asibitoci na marasa lafiya da kuma yadda fyade ya zama ruwan dare
Yau 28 ga Watan Janairu 2025 wa'adin ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar ECOWAS ke cika a hukumance. Shekara guda kenan bayan da suka sanar da ballewa daga kungiyar da suke zargi da taka rawa da bazar Faransa
Birane kamar su Abala Tanout Tahoua Zinder da Yamai na daga cikin irin wadanan wurare da sufetoci masu aikin bincike suka gano an handame daruruwan million cfa kamar yadda ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya bayyana
A daren jiya lahadi ne kungiyar ‘yan tawayen M23 mai gwagwarmaya da makamai da sojojin Rwanda suka kutsa kai zuwa tsakiyar birnin Goma bayan shafe makonni suna tunkararsa daga lardin Kivu na Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo.
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke huldar diflomasiyya da Rwanda yayin da ake gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda da dakarun gwamnatin a kusa da muhimmin birnin Goma na gabashin kasar.
Wani harin jirgi mara matuki a kan asibiti daya da ya rage yana aiki a El-Fasher a yankin Darfur na kasar Sudan, ya kashe mutane 30 kana ya jikata wasu da dama, a cewar wata majiyar kiwon lafiya a yau Asabar.
Za a soke bukatar neman iznin tafiye-tafiye ga ilahirin ‘yan Afrika, in banda ‘yan kasashen Somaliya da Libya, saboda dalilai na tsaro.
A wanan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar warware sabani da zuba jari da ake kira CIRDI inda yake neman a biyashi diyya dai dai da asarar da ya tafka a mahakar Uranium da ke arewacin Nijar
A cewar Ministan tsaron Nijar, an tanadi motoci da jirage da makaman yaki sannan hafsoshin kasashen uku na tattaunawa da juna kuma tuni suka kammala tsara yadda ayyukan rundunar za su gudana.
A wani al'amari mai matukar bakanta rai, arangamar da ta kaure tsakanin mahaka ma'adinai ba bisa ka'ida ba da jami'an tsaro a Ghana ta yi ajalin takwas daga cikinsu.
Domin Kari
No media source currently available