A karshen Janairun 2024 ne wadanan kasashe suka ba da sanarwar ficewa daga kungiyar CEDEAO saboda zargin shugabaninta da yin katsalandan a harkokin cikin gidansu, kuma yunkurin mayar da su cikin kungiyar ya ci tura, to amma sabon matsayin na AES alama ce da ke nuna an fara samun sassaucin ra'ayi.
A karshen taron da suka gudanar a ranakun Asabar 22 da Lahadi 23 ga watan Fabairun 2025 a birnin Bamako, minstocin kasashen Nijar Mali da Burkina Faso wadanda suka hada da na tsaro da na harakokin waje, da na kudade da na makamashi da na hanyoyin sufuri sun fara da bayyana gamsuwa da tasirin ayyukan hadin guiwar da dakarun kasashen uku ke gudanarwa da sunan yaki da ta’addanci.
Kasashen uku sun ce suna mutunta dangantaka ta jini, amintaka da hulda da kasashen Afirka ta yamma, lamarin da ke bai wa al’ummomin CEDEAO ‘yancin kai da kawowa a yankin AES.
Dangane da batun fara tattaunawa biyo bayan wasikun da suka aike wa shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS, kasashen na AES sun jaddada aniyar mutunta tsare-tsare da hanyoyin da za a yi amfani da su domin tabbatar da jin dadin al’ummominsu da na sauran kasashen baki daya.
Taron ministocin na AES ya ce ya kammala hada wani kundimai kunshe da manufofin da kasashen uku ke fatan ganin an yi wannan tattaunawa a karkashinsu.
Koda yake ta yaba da wannan yunkuri kakakin kungiyar M62 Falamta Taya na cewa akwai bukatar neman jin ra’ayin talakawa kafin shiga ko wane irin zama da wata kungiya.
Kawo yanzu ba wata amsa daga bangaren kungiyar kasashen Yammacin Afirka a hukunce dangane da tayin na kasashenAES, wanda a ra’ayin Souley Oumarou yin na’am da sabon matsayin na kasashen Sahel shine mataki mafi a’ala ga jama’ar kungiyoyin biyu.
Bayan da suka fitar da tambarin kungiyarsu a karshen watan Disamban bara kasashen AES sun bullo da tutar kungiyar wanda ke da rinjaye launin tsanwa da wani tambari mai launin kore da ja da ruwan goro a tsakiyarsa.
Shugaban Mali, shugaban rikon confederation AES Janar Assimi Goita ne ya jagoranci kwarwaryan bukin yaye labulen sabuwar tutar a karshen taron ministocin kasashen uku.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna