Daftarin ya kuma yi kira ga sojojin Rwanda da su daina taimakawa kungiyar M23 kana su gaggauta janyewa daga DR Congo ba tare da gindaya wasu sharuda ba.
Kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun ce a zahiri Rwanda ce take iko da kungiyar ‘yan tawayen M23 kuma akwai akalla dakarunta 4, 000 da ke yaki tare da su.
Yau aka kammala babban taro na kasa a jamhuriyar Nijar bayan shafe kwanaki 5 na tattauna hanyoyin mafitar matsalolin da kasar ta tsinci kanta a ciki a tsawon gomman shekarun da suka gabata
Tun bayan kwace iko da garin Bukavu, dakarun sojin Congo da ke janyewa suka kare da gwabza fada da kungiyar ‘yan bindigar da ke kawance dasu da ake kira da Wazelendo wacce ke adawa da janyewar.
“Dukkanninmu mun yi matukar damuwa a game da yiwuwar hadarin fadawa cikin yaki gadan gadan a yankin saboda abin da ke faruwa a DRC
Harin RSF a kan jihohin Al-Kadaris da Al-Khelwat dake gabar kogin Nilu - masu tazarar kimanin kilomita 90 daga babban birnin kasar - ya tilastawa dubban mutane arcewa daga gidajensu, kamar yadda ganau suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mahalarta babban taron kasa a Nijar na ci gaba da tafka muhawara tare da bullo da shawarwarin da suke fatan ganin an shigar da su a kundin tsarin mulkin rikon kwaryar kasar a ci gaba da yunkurin mayar da ita kan tafarkin dimokradiyya
Al’ummar Jamhuriyar Nijar da ke zaune a Najeriya sun ce a yanzu sun fi ganin amfanin mulkin soja da na farar hula musamman a bangaren tsaro
Wasu manyan jagororin yankin Tigray na kasar Habasha na kiran da a aiwatar da dukkan matakai na yarjejeniyar Pretoria.
Akalla mutum 48 ne suka mutu sakamakon rugujewar wata mahakar zinare da ake aiki ba bisa ka’ida ba a yammacin kasar Mali a ranar Asabar, kamar yadda hukumomi da majiyoyin yankin suka shaida wa kamfanin dillanci labaran Faransa.
A ranar Asabar fargaba ta mamaye bakin dayan birnin mafi girma na biyu a gabashin Congo inda dubban mazauna yanki suka tsere cikin kaduwa yayin da kungiyar ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kara dannawa a cikin yankin.
‘Yan kasar Afirka ta Kudu farar fata sun nuna goyon bayansu ga shugaba Donald Trump a yau Asabar, inda suka taru a ofishin jakadancin Amurka da ke Pretoria, inda suka yi ikirarin cewa gwamnatinsu ta nuna musu wariyar launin fata.
Domin Kari
No media source currently available