Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mako Mai Zuwa Za Mu Aiwatar Da Shirin Haraji Akan Canada, Mexico - Trump


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

“Saka harajin ya zama wajibi, saboda kasashe da dama ba sa kyauta mana, ciki har da kawayenmu da abokan hamayyarmu.” In ji Trump.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai sakawa kayan da ake shiga da su kasar daga Canada da Mexico harajin kashi 25 a mako mai zuwa kamar yadda ya tsara a baya, yana mai cewa kasashen wadanda makotan Amurka ne ba sa wani abin a-zo-a-gani wajen dakile kwararar miyagun kwayoyi cikin Amurka.

Trump ya kuma fada a dandalin sada zumunta na Truth Social da ya mallaka cewa, zai sake sakawa China wani karin haraji da kashi 10 a ranar Talata mai zuwa kan kayayyakin da ake shiga da su Amurkar daga kasar – wato kari akan kashi 10 da ya saka mata a farkon watan nan.

“Saka wadannan haraji ya zama dole, saboda kasashe da dama ba sa kyauta mana, ciki har da kawayenmu da abokan hamayyarmu.”

Ba tare da bata lokaci ba, China ta yi maza ita ma ta sakawa Amurkar haraji kwatankwacin yadda Amurka ta saka mata.

A farkon watannan mai karewa ne Trump ya sakawa Canada da Mexico haraji, wadanda su ne abokanan huldar cinikayyarta na kut-da-kut.

Sai dai ya jinkirta fara aiwatar da wannan shiri zuwa hudu ga watan Maris bayan da Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum ta ce za ta tura dakaru dubu 10 zuwa iyakar arewacin kasar don taimakawa wajen yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG