Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Sudan Sun Kwato Birnin Obeid Daga Hannun RSF


Sojojin Sudan Suna Muryana
Sojojin Sudan Suna Muryana

Jami’ai sun ce sojojin Sudan a ranar Lahadi sun yi nasara a kawo karshen kawanya ta sama da shekara guda a kan muhimmin birnin Obeid, inda suka maido da hanyar shiga wani muhimmin yanki a kudu maso tsakiyar kasar.

Dakarun Sudan sun kuma karfafa muhimman hanyoyin fitar da kayayyaki a cikin kusan shekaru biyu da suka kwashe suna yaki da dakarun sa kai na RSF.

A cikin wata sanarwa da ya fitar kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Nabil Abudllahi ya ce, sojojin sun kuma fatattaki dakarun RSF daga tungarsu ta karshe a lardin kogin Nilu a wani koma baya ga dakarun sa kan.

Sudan ta fada cikin rikici a cikin watan Afrilun bara, lokacin da tankiya tsakanin sojoji da dakarun RSF ta rikide zuwa yakin basasa a fadin kasar.

Yakin da ya lalata babban birnin kasar, Khartoum, da sauran garuruwa, ya yi fama da munanan laifuka da suka hada da yawan fyade da kuma kashe-kashe kabilanci da suka kai matsayin laifuffukan yakin da cin zarafin bil adama, musamman a yammacin yankin Darfur, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

Kakakin rundunar sojin Abdullahi ya ce dakarun soji a yankin al-Sayyad sun yi nasarar bude hanyar zuwa birnin Obeid tare da kawo karshen kawanya da dakarun RSF suka yi wa birnin, wanda ke zama babban birnin lardin Kordofan ta Arewa.

Garin yana dauke da filin saukar jiragen sama da kuma runduna ta 5 na sojoji da aka fi sani da Haganah.

Obeid da ke zama cibiyar kasuwanci da sufuri, tana kan hanyar jirgin kasa da ta hada Khartoum zuwa Nyala, babban birnin lardin Darfur ta Kudu. Dakarun RSF sun yi wa garin kawanya tun farkon rikicin da ya barke a watan Afrilun 2023.

Ministan Kudi Jibril Ibrahim ya yaba da ci gaban da sojojn suka samu a Obeid a matsayin wani “babban mataki” na rusa kawanyar da RSF ta yi wa Al-Fasher, babban birnin lardin Darfur ta Arewa, da kuma kai kayan agaji ga yankin Kordofan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG