Mutane 46 sun hallaka sa’ilin da wani jirgin saman sufurin rundunar sojin Sudan ya rikito a wata unguwar zaman mutane dake wajen birnin Khartoum, kamar yadda gwamnatin lardin ta bayyana a yau Laraba.
Jirgin saman kirar Antonov ya fadi ne a daren jiya Talata a kusa da sansanin sojan sama na Wadi Seidna, daya daga cikin cibiyoyin soja mafi girma dake yankin Omdurman, dake arewa maso yammacin babbn birnin kasar.
Rundunar sojin, wacce ke gwabza yake da kungiyar ‘yan tawayen rsf tun cikin watan Afrilun 2023, tace ya rikito ne sa’ilin da yake kokarin tashi, inda ya hallaka tare da jikkata sojoji da fararen hula.
“Bayan kididdigar karshe, adadin wadanda suka yi shahada ya kai mutane 46, inda 10 suka jikkata,” kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin lardin Khartoum ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Haka kuma fadowar jirgin ta sabbaba daukewar wutar lantarki a unguwannin dake kusa da wurin tare da lalata gidaje da dama a yankin.
Dandalin Mu Tattauna