Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar (III) ya sanar da gnina jinjirin watan domin fara azumin Ramadan.
Shugaban Majalisar Koli ta harkokin addinin Musulunci ne ya sanar da hakan a wani sako da aka yada a yau Juma ‘a.
Sarkin Musulmin yace za a fara azumin watan Ramadana a Najeriya a gobe Asabar.
An ruwaito shi yana cewar, "yau, Juma'a, 28 ga watan Fabrairun 2025, wacce ta zo daidai da 29 ga watan sha'aban shekarar, 1446, bayan hijirar, an bamu rahoton ganin jinjirin watan ramadan a fadin Najeriya."
"Mun tantance tare da tabbatar da sahihancin rahotanin, don haka gobe 1 ga watan Maris ta kasance 1 ga watan ramadan na shekarar 1446 bayan hijira."
Sanarwar Sarkin Musulmin na zuwa ne sa'o'i bayan da kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan.
Shafin Haramain Sharifain ya ruwaito ganin jinjirin watan Ramadan a Saudiyya, inda ya ce, "an ga jinjirin watan Ramadan na shekarar 1446 wato shekarar 2025 a Saudiyya."
Hakazalika, a Jamhuriyar Nijar, Fariminista Ali Mahamane Lamine Zaine ne ya sanar da ganin jinjirin watan da maraicen ranar Juma'a a gidan talabijin na kasa
Cikin wata sanarwa fraiministan na Nijar lamine zaine ya karanta ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.da suka hada da zinder da kuma diffa
Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446.
Dandalin Mu Tattauna