Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Likitoci Marasa Shinge Ta Dakatar Da Aiyukan Ta A Sansanin Zamzam Na Sudan


Tambarin likitoci marasa shinge
Tambarin likitoci marasa shinge

Likitoci marasa shinge sun dakatar da aiyukan su a yakin da fari ya yiwa katutu na sansanin Zamzam a Sudan sakamakon karuwar hare hare da rikici a yankin.

A ranar Litinin likitoci marasa shinge suka dakatar da aiyukan su a yakin da fari ya yiwa katutu na sansanin Zamzam a Sudan sakamakon karuwar hare hare da rikici a yankin.

Kungiyar bayar da agajin likitocin ta duniya, da aka kuma sani da sunan ta na Faransanshi da Medecins Sans Frontiere MSF, ta ce, fada tsakanin sojojin Sudan da abokan hamayyar su na dakarun kad ta kwana ya karu a sansanin dake arewacin Darfur.

Karuwar rikicin yasa da wahala kungiyar ta samar da aiyukann jin kai na ceto rayuwar dubban mabukatan da aka daidai ta a yankin, cewar kungiyar a cikin wata sanarwa, inda ta kara da cewa, ta dakatar da duk aiyukan ta a Zamzam da ya hada da asibitin ta.

Shugaban aiyyukan kungiyar a Sudan Yahya Kallilah ya ce, dakatar da aikin su a daidai lokacin da tashin hankali ke kara rincabewa a Zamzam, abin takaici ne.

Kallilah ya kara da cewa, kasancewa kusa da inda ake tashin hankali, da fuskantar wahalhalu wajen aika kayayyaki, da fuskantar matsala wajen aika kwararrun ma’aikata, da rashin tabbas a hanyoyin fita daga sansanin, yasa MSF zabin ta kadan ne.

Sudan ta tsunduma cikin yaki ne lokacin da aka fara fada a watan Apirilun shekarar 2023 tsakanin sojoji da RSF, bayan daukar dumi. Sakamakon rikicin da ya barke a babban birnin kasar Khartoum, da ya watsu zuwa wasu sassan kasar.

Rikicin da ya kashe sama da mutane 24,000, ya tilasta wasu mutanen milyan 14 ficewa daga gidajen su, lamarin da ya haifar da fari a sassan kasar dabam dabam.

Rikicin da ake yi a Zamzam ya rincabe ne a ranar 11-12 ga watan Fabrairu, a cewar kungiyar ta MSF. Asibitin dake wurin ya karbi marasa lafiya da aka jikkata su 130, mafi yawan su da raunin harbin bindiga da munanan raunuka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG