Akalla mutum 11 aka tabbatar sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata a birnin Bukavu da ke gabashin Congo bayan da aka samu wata fashewa a wani gangamin da shugabannin ‘yan tawayen M23 suka shirya.
A farkon watan Fabrairu kungiyar ta M23 ta karbe ikon Bukavu birni na biyu mafi girma da ya koma karkashin ikonta.
Shugabannin ‘yan tawayen na zargin gwamnatin Congo da haddasa fashewar suna masu cewa wadanda suka kai harin na cikin wadanda suka mutu.
Akwai dai rahotanni mabanbanta a tsakanin ‘yan tawayen da jami’ai kan adadin mutanen da suka kai hari da wadanda suka mutu.
Gwamnatin Congo ta dora alhakin harin akan abin da ta kira “dakaru na waje.”
Dandalin Mu Tattauna