Yayin da Janhuriyar Nijar ke dada daukar tsauraran matakai kan harkokin shigi da fici, ta na kuma sassauta ma bakin da ke cikin kasar
A yau Alhamis Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar jihohi 2 a kudancin Sudan “na gab da afkawa cikin bala’i” bayan da rahotanni suka bayyana cewar barkewar sabon rikici a daya daga cikin biranensu ya hallaka akalla mutane 80.
Luguden wutar da jiragen sojan sama suka yi a washegarin faruwar wannan al’amari ya bada damar hallaka ‘yan ta’addan 15 tare da raunata wasu masu tarin yawa.
Ga dukkan alamu, yakin Janhuriyar Demokaradiyyar Congo na dada kazancewa duk da kokarin da ake na kira ga bangarorin da ke fadan.
Kungiyar ICRC wadda gwamanatin Nijar ta dakatar da ayyukanta , ta fara aiki ne tun shekarar 1990 inda ta ke gudanar da ayyukan jinkai kamar a fannin kiwon lafiya da kuma fannin kula da ‘yan gudun hijira da wuraren da ake fama da matsalolin tsaro da kawo tallafi ga mutanen da wani iftila’i ya shafa
Koda yake ba a bayyana dalilan yin haka a hukunce ba kwararru a harkar yaki da cin hanci na alakanta matakin da rashin gamsuwa da ayyukan hukumar, kuma a cewarsu har yanzu da sauran gyara muddin da gaske ake yakin.
Sanarwar da gamayyar kungiyoyin siyasa da na soja da ake kira da “kawancen kogin Congo” wanda M23 ke zama mamba ta fitar da maraicen jiya Litinin, tace za’a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta yau Talata a “bisa dalilai na jin kai.”
Malakar kasa batu ne da ke yawan janyo takaddama a Afrika ta Kudu, inda farar fata ke ci gaba da mallake galibin gonakin kasar shekaru 30 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
Shugaban hukumar Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka Dr Omar Alieu Touray, ya sanar cewa ya sami wasikun bukatar tattaunawa daga kasashe 2 cikin mambobin kungiyar AES 3, duk da cewa tuni al’umomi da hukumomin kasashen suka yi bukin tabbatar da ficewarsu a hukumance.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kai farmakin a ranar Asabar a shafukan sada zumunta, yana mai bayyana lamarin da auna "Babban mai shirya kai hari na ISIS da sauran 'yan ta'addan da ya dauka kuma yake jagoranta."
Domin Kari
No media source currently available